Shin Kun San Kyautan Nawa Tawagar Da Ta Lashe Kofin Nahiyar Afirka Za Ta Samu?

Duk tawagar da ta lashe gasar cin kofin nahiyar Afirka ta 2024 za ta samu kyautar dala miliyan bakwai ($7M), kwatankwacin (Yuro Miliyan 6.4), kamar yadda Hukumar Kwallon Kafar Afirka ta CAF ta bayyana a cikin wata sanarwa a ranar Alhamis.