Shekara na biyu ban yi ido hudu da mijin da ya aure ni ba, sai dai kanni da abokansa su zo su kwana da ni su yi tafiyar su – Wata Mata

A yankin Kudu maso Gabashin kasar nan akwai wata al’ada da ƴan ƙabilar inyamurai ke yi inda sukan tilastawa ƴaƴan su mata auren mazajen da suka girme su da shekaru masu yawa saboda da kawai yarinya ta yi ciki ba da aure ba.

Wannan al’adan na da nasaba ne da irin fifikon da iyamurai suke baiwa maza fiye da mata.

A ganin su namiji ko mace bai cika mutum ba idan ba shi da Ɗa namiji.

A dalilin haka ya sa tsoho ko tsohuwa za su auri mace budurwa da ta dauki cikin da bata so domin su rike ɗan a matsayin nasu.

Sannan a al’adan iyamurai babu dan da za a haifa da ba shi da Uba dole sai an nemo masa uba koda cikin yaron ba ayi shi cikin aure ba.

Auren dole

Chinwe Eze mahaifiyar Yara biyu mace da namiji ta bayyana yadda ta auri mijinta mai shekara 65 a lokacin da take da shekara 16.

Ta ce ta auri tsohon ne bayan da wani saurayinta ya dirka mata ciki.

Chinwe ta ce a lokacin da ta yi ciki tana zaune a gidan kawunta dake Aba jihar Abia saboda iyayenta basu da kudin kula da ita da kannenta biyar.

“Saboda rashin kudin da zai kula da ni da dan dake ciki na saurayi na ya biya kawuna Naira 20,000 sannan na koma gida wajen iyaye na.

“Ko da na koma gida mahaifina ya aurar da ni wa wani tsoho mai shekara 65 inda bayan shekara daya da auren ya rasu.

“Da na kammala takaba sai na dawo gida amma sai na ƙasa kula da dana saboda tallauci. ‘Yan uwan mijina sun ba ni zabi cewa za su kula da ni da dan da na haifa idan na dawo na ci gaba da haifan musu ‘ya’ya da kannen mijina ko Kuma na zauna cikin talauci a gidan mahaifina.

“Haka nan na koma gidan mijina da zama na ci gaba da haihuwa duk da haka kannen mijina da ‘yan uwansa basu kula da ni.

Ngozi Asogwa

Wata mazauniyar Nsukka jihar Enugu Ngozi Asogwa ta bayyana cewa ta auri wani mutumi da har yau bata taba ganin shi Ido da ido ba saboda wata mata ta kaita da iyayenta ta baro.

Ngozi ta ce ta auri mijinta tana da shekara 17 bayan ta yi ciki.

Ta ce matan ta tabbatar wa iyayenta cewa dan uwanta zai kula da ita da dan dake cikinta idan ta yarda ta aure shi.

“Bayan da na haihu sai na tare gidan ‘yar uwan mijina. Sai dai na yi tsawon shekara biyu ina zaune ban taɓa saka shi a ido ba, wato shi mijin nawa.

“Da na tambayi matar sai ta ce aiki ne ya yi wa masa yawa a Onitsha shiya ya sa bai zo ba.

“Daga baya na samu labarin cewa ashe kaimu aka yi aka baro. Na kira sa awaya bayan na samu lambar wayar sa sai ya bayyana mun cewa yana fa da aurensa, ni an auro ni ne domin in rika haifa musu ‘ya’ya da wasu mazajen.

Ngozi ta ce Ƴar uwan mijinta ta bata zabi ko ta zauna ta ci gaba da haifa musu yara ko ta biya Naira 273,000 kudin sadakin da ta biya a kanta.

Kosarachi Amadi

Ita ko Kosarachi Amadi mazauniyar Umunachi jihar Anambra ta ce da saninta ta amince ta auri mace tsohuwa domin ta rika haifan mata yara.

Kosarachi ta ce tun da tsohuwar ta yi aure ba ta taba haihuwa ba har mijinta ya mutu.

Ta ce tsohuwar ta yi alkawarin kula da ita ta kuma karbi dan dake cikinta a matsayin nata idan ta amince za ta rika haihuwa mata yara.

“Mahaifiyata cikin shege ta yi ta haife ni sannan na san wahanan da nake sha wajen mutane saboda yadda aka haife ni.

“A dalilin haka ya sa da na dauki ciki na amince na rika kwana da maza domin na haifi ‘ya’yan wa tsohuwan da ta biya kudin sadakina.

Kamuwa da cututtuka

Shugaban wata kungiya mai zaman kanta dake jihar Anambra ‘Shoulder for Gender Support and Development Initiative (SGSDI)’ Chioma Okeke ta ce aure irin haka akan yi shi ne da yarjejeniyar cewa budurwar za ta rika haihuwar yara tana kwana da mazaje daban-daban babu komai, sannan namiji ko mace da ta aure ta za ta rika kula da ita.

Okeke ta ce matan da suka yi irin wannan aure basu taba rabuwa da tallauci sannan yana jefa su cikin mummunar hadarin kamuwa da cututtuka kamar cutar sanyi ko Kuma kanjamau.

Ta ce wayar da kan mutane game da illar dake tattare da aure irin wannan da koyar da darasin haihuwa, daukan ciki, bada tazarar haihuwa ga dalibai na cikin matakan da zai taimaka wajen guje wa aukuwar abubuwa irin haka.

Okeke ta yi kira ga malaman addini da su taimaka wajen wayar wa da mutane kai sanin illar yin irin wannan aure.

Matakan shawo kan matsalar da gwamnati ta dauka

Shugaban kwamitin zantar da dokar kare hakin yara kanana ta jihar Anambra Hope Okoye ta ce gwamnati na kokari wajen ganin dokar kare hakkin yara na aiki a jihar.

Hope ta Kuma ce gwamnati za ta hada hannu da kananan hukumomi da sarakunan gargajiya domin wayar da kan mutane sanin illolin da ke tattare da tilasta wa mata yin irin wannan aure.