SHARI’AR ZARGIN SHETTIMA YA FITO TAKARA WURI BIYU: Kotu ta kori ƙarar da PDP ta nemi a soke takarar Tinubu da Shettima

Kotun Ɗaukaka Ƙara ta kori wata ƙarar da PDP ta shigar tun kafin zaɓe, inda ta nemi a soke takarar Bola Tinubu na APC da ɗan takarar mataimakin sa, Kashim Shettima.
PDP ta nemi a soke takarar ta su, saboda ta yi zargin Shettima ya fito takara wuri biyu a lokacin zaɓen fidda-gwanin jam’iyyar APC.
A wancan lokacin dai Kotun Tarayya ta kori ƙarar bisa dalilin cewa PDP ta kasa gabatar da cikakkar hujja mai nuna cewa Shettima ya fito takarar Sanatan Barno ta Tsakiya, kamar yadda ta yi ƙorafi.
PDP ta ce Shettima ya karya doka, don haka bai kamata shi da ɗan takarar shugaban ƙasa Bola Tinubu su tsaya takara ba.
A wancan lokacin, Mai Shari’a na Babbar Kotun Tarayya, Inyang Ekwo ya kori ƙarar da PDP ta shigar. Ganin haka sai PDP ta garzaya Kotun Ɗaukaka Ƙara, inda har aka yi zaɓe ba a yanke hukunci a Kotun Ɗaukaka Ƙara ba.
A ranar 24 Ga Maris, Kotun Ƙoli ta kori ƙarar, tare da cewa hukuncin da Babbar Kotun Tarayya ta yanke ya na nan daram. Saboda PDP ta kasa kawo hujjar da za ta nuna cewa Shettima ya fito takarar sanata a lokaci guda.
Tun cikin watan Yuli 2022 PDP ta shigar da ƙarar, amma sai ranar Juma’a aka yanke hukunci.
Kotun Ɗaukaka Ƙara ta yi watsi da PDP tare da amincewa da wani bayanin da babban lauyan Tinubu da Shattima ya yi, inda ya ce PDP ta ƙi fuskantar sha’anin cikin gidan ta, ta koma ta na leƙe-leƙe cikin lamarin cikin gidan APC.
Da ya ke jawabi a madadin sauran alƙalai biyu da su ka yanke hukuncin, Mai Shari’a Abundaga ya ce PDP ta kasa kafa hujja kan zargin da ta ke yi wa Shettima.
A yanzu dai akwai sauran ƙararrakin da za a ci gaba waɗanda Atiku da Obi da PDP da LP da ma wasu jam’iyyu su ka shigar kan zargin murɗiya, aringizo da ƙin amfani da BVAS a tura sakamakon zaɓen shugaban ƙasa a manhajar iRev domin kowa ya ga sakamakon a duk inda ya ke.