SHARI’AR HARƘALLAR YI WA CIYAWA FITIKIN NAIRA MILIYAN 544: Kotu ta ƙi amincewa da shaidun da EFCC ta gabatar don a ɗaure Babachir Lawal

Mai Shari’a Charles Agbaza na Babbar Kotun Abuja ya yi fatali da hujja da shaidar da Hukumar EFCC ta gabatar a shari’ar da ake tuhumar tsohon Sakataren Gwamnatin Tarayya, Babachir Lawal.
Ana tuhumar Babachir tare da ƙanin sa Hamidu da wasu mutane da kamfanoni da harƙallar karkatar da kuɗaɗen kwangilar nome ciyawa a Arewa maso Gabas har Naira miliyan 544.
Dukkan waɗanda ake tuhumar dai ba su amsa laifin da ake zargin sun aikata ba.
Da ya ke yanke hukunci, Mai Shari’a ya amince da uzirin waɗanda ake tuhuma cewa, cikin 2021 kotu ta ƙi yarda da wasu shaidun da aka ce an hujjoji ne aka samu a waya.
Mai Shari’a ya ce EFCC ta gabatar masa hujjojin da kotu ta yi watsi da su a baya.
Ya ce duk wasu hujjojin kalaman da aka fitar daga waya, waɗanda aka yi watsi da su a baya, sun zama tatsuniya kawai.
“Na bi bayanan tankiyar da ke tattare da wannan shari’a, na gano cewa batutuwa biyu ne kaɗai abin dubawa.
“Da farko, shin shaidun EFCC duk ji-ta-ji-ta ce kawai, ko kuma shin a baya kotu ta taɓa yin watsi da su.
A batu na farko dai wanda ke bada shaidar ya shaida wa kotu yadda EFCC ta gayyace shi ofishin ofishin ta, har cikin ɗakin gwaji, aka nuna masa wasu bayanai daga waya samfurin iPhone7.
“A nan zan yarda cewa mai shaida ba shi ne ya yi bayanan ba, shi ma nuna masa kawai EFCC ta yi.
“Don haka duk abin da mai shaida ya faɗa, shi ma faɗa masa aka yi, don haka ji-ta-ji-ta ce kawai. Saboda haka na bai wa wanda ake tuhuma gaskiya.
“Batu na biyu kuwa wannan shaida da aka bayar, kotu ta taɓa yin fatali da su. Kuma a zaman yanzu an ɗaukaka ƙarar yin fatali da shaidun a Kotun Daukaka Kara.” Inji Mai Shari’a.
A makonni biyu da suka gabata ne dai lauyan su Babachir Lawal, mai suna Aikin Olujimi ya ƙi yarda da shaidun EFCC waɗanda wani mai suna Dare Folarin ya gabatar daga wata waya samfurin iPhone7 daga wani Musa Bulani.
Lauya Olujimi ya ce EFCC ta yi ƙoƙarin yin sumogal ɗin shaidun da kotu ta yi watsi da su a baya.
Sauran waɗanda ake tuhumar duk sun yarda da matsayar ɓangaren Babachir Lawal ya gabatar.
Sai dai kuma zaman kotun bai yiwu ba, an ɗage ci gaba da shari’ar zuwa ranar 16 da 17 Ga Fabrairu.