Sanatan da aka zarga ya tafka harkallar ayyukan talakawan shiyyar sa, ya maye gurbin marigayi Ibrahim a Zaben Jigawa

Sanata Sabo Muhammad ya maye gurbin marigayi Tijjani Ibrahim wanda ya Allah yayi wa rasuwa bayan yayi nasara a zaben fidda gwani na kujerar sanatan Shiyyar Jigawa ta Kudu a karkashin APC.
Sanata Tijjani Ibrahim ya rasu ranar 13 ga Agusta.
Sanata Ngudu wanda shine yake wakiltar shiyyar a majalisar dattawa ya sake tsaya bayan rasuwar Ibrahim Tijjani. Shine kuma dan takara daya tilo da ya tsaya takara a zaben. Ya sami kuri’u 361.
Idan ba a manta ba Hukumar ICPC ta zargi Sanata Sabo da tafka harkallar kwangilolin samar da ababen more rayuwa ga al’ummar shiyyar sa.
Hukumar ta zargi Sanatan da yin sama da fadi da kudaden ayyukan mazabar sa da kuma yin harkallar raba kwangiloli ga kamfanonin ‘yan uwansa.