SALLAH: Matawalle ya yi liyafar cin abincin sallah da marayu a gidan Gusau

Gwamnan Jihar Zamfara Bello Matawalle yayi liyafar bikin sallah da wasu marayu a fadarsa dake gidan gwamnati a Gusau.

Yusuf Idris, maitaimakawa gwamnan kan harkar yaɗa labarai ya shaidawa PREMIUM TIMES HAUSA cewa gwamna Matawalle ya tsara bikin cin abincin ne da marayu kamar yadda iyaye suke yi da ‘ya’yansu da bikin sallah domin ya karrama marayun.

Jihar Zamfara tana daya daga cikin jahohin Nageriya dake da yawan yara marayu sakamakon ayyukan yan ta’adda yan bindiga masu kisa da satar dabbubi.

Gwamna Matawalle yace marayun ƴaƴan sane kuma gwamnatinsa zata cigaba da taimaka masu iya gwargwadon iko.

” Ni ne ubansu, zai kasance tare dasu a koda yaushe, kuma gwamnatina zata cigaba da tallafa masu da biya musu bukatunsu. Allah ne ya kaddara cewa zasu zama marayu ba don suna so ba bai kamata a yi watsi dasu ba”

Gwannan yace tallafawa marayu hakkin al’umma ne baki daya saboda babu wanda yasan abinda gobe zata haifar.

Daga nan sai yayi kira ga masu hannu da shuni da su tallafawa marayu da marasa karfi dake a jihar domin samun rabauta gobe kiyama

Yace gwamnatinsa zata yi duk mai yiyuwa wajen kula da ilimin marayun saboda suma suna da hakki kamar kowane yaro dake cikin Jihar ta Zamfara.

Matawalle yayi kira ga marayun da suyi addu’a domin samun zaman lafiya a Jihar da kuma Najeriya.