SABODA TIWITA: Sanatocin PDP sun fice daga Zauren Majalisar Dattawa

Majalisar Dattawa ta yi shiru ba ta ce komai ba, bayan da Sanatocin jam’iyyar PDP su ka fice daga zaman Majalisa, saboda nuna rashin goyon bayan kulle amfani da Tiwita wanda Gwamnatin Shugaba Buhari ta yi.

Shirun da Majalisar Dattawa ta yi ya sha bamban da irin matakin da Majalisar Tarayya ta dauka, wadda ta yanke shawarar cewa za ta gayyaci Ministan Yada Labarai, Lai Mohammed ya bayyana a gaban ta.

Kuma Mambobin Majalisar Tarayya na PDP sun fice daga Majalisa, bayan da Kakakin Majalisa ya hana a gabatar da korafin kiran Shugaba Buhari ya canja tunanin kulle Tiwita da gwamnatin sa ta yi.

Kalaman da Ministan Shari’a Abubakar Malami ya yi cewa za a gurfanar da wadanda su ka karya doka, bai hana manyan masu rike da mukamai ‘yan APC ci gaba da amfani da Tiwita ba.

An yi tsammanin Majalisar Dattawa za ta tattauna batun, amma sai ta yi shiru.

Gwamnatin Najeriya dai ta gindaya sharudda kadin ta sake bude Tiwita.

Gwamnatin Najeriya ta bayyana cewa za ta sake bude Tiwita idan kamfanin ya tabbatar wa kasar nan cewa ba zai rika watsa shiririta da soki-burutsun da zai haddasa fitina ba.

Ministan Harkokin Kasashen Waje, Geoffrey Onyeama ne ya bayyana haka a lokacin ganawar sa da wasu jakadun kasashe na nan Najeriya.

Ya ce duk da dai ba zai iya cewa ga ranar sake budewa ba, amma dai babban sharadi shi ne a matsayin Tiwita na soshiyal midiya, ta tabbatar ta kasance kafar yada abin alheri da alfanu, ba sharri ba.

“Matsawar aka ce ka na da karfin da za ka iya isar da sakonni, to ya kamata ka rika gudanar da wannan sana’a a cikin mutunci ba da cin zarafi ko kokarin haddasa fitina a kasa ba.” Haka Onyeama ya shaida wa manema labarai.

“Ba mu ce Tiwata na yi wa kasar nan wata barazana ba, a’a. Mun dakatar da saboda kawai sun bari ana amfani da su domin a kawo rudun da ka iya hargitsa kasa ko kafar aikata muggan laifuka.”

Ya ce abinda gwamnati ta zartas na daga cikin muhimman batutuwan da su ka shafi tsaron kasar nan.

“Saboda idan Babu tsaro, to duk gaba daya ne duk za mu yi asara.

Tuni dai kungiyar SERAP ta yi barazanar za ta ƙalubalanci Gwamnatin Buhari a kotu.

Kungiyar SERAP ta ce hana amfani da kafar soshiyal midiya ta twitter da Gwamnatin Shugaba Muhammadu ta yi, haramtacce ne, kuma ƙungiyar ta ce za ta gaggauta maka gwamnatin tarayya kotu.

SERAP ta bai wa gwamnatin tarayya wa’adin sa’o’i 48 ta janye dakatarwar da ta yi wa Twitter, ko kuma ta maka ta kotu kai-tsaye.

A ranar Juma’a ce Ministan Yaɗa Labarai Lai Mohammed ne ya bayyana dakatar da twitter daga amfani a Najeriya har sai yadda hali ya yi.

Kaakin Yaɗa Labarai na Minista Lai, Segun Adeyemi ne ya sanar da haka a ranar Juma’a, a cikin wata sanarwa da ya fitar a madadin ministan.

Sai dai kuma jim kaɗan bayan fitar da sanarwar, SERAP a fusace ta kira dakatarwar haramtacciya, kamar yadda Mataimakin Daraktan SERAP, Kolawole Olueadare ya bayyana a cikin wata sanarwa da ya fitar a yammacin ranar Juma’a.

“Dakatar da twitter a Najeriya tauye wa ‘yan Najeriya ‘yancin faɗar albarkacin bakin su ne da kuma toshe masu wata muhimmiyar kafar samun bayanai da aika saƙonni.

“Wannan dakatarwar wani salo ne aka yi amfani da shi na azabtar da mutane bai-ɗaya a lokaci guda. Hakan ya saba wa tsarin dokokin ƙasa-da-ƙasa.

“Saboda haka mu na kira ga Shugaba Buhari ya gaggauta janye wannan dakatarwar, cikin sa’o’i 48 ko kuma mu da shi mu haɗu a kotu, saboda ya danne haƙƙin jama’a masu tarin yawa.