RANAR ZAZZABIN CIZON SAURO: Dalilin da ya sa cutar ta yi wa tsanani a yankin Afrika – Kwararru

Kwararru sun bayyana cewa rashin ware kudade domin gudanar da bincike kan dakile yaduwar zazzabin cizon sauro na daga cikin dalilan da ya sa yaduwar cutar ta yi wa yankin Afrika tsanani.

Wani farfesa a fannin inganta muhalli a Jami’ar Oye-Ekiyi Azeez Olaniya ya koka kan yadda shugabannin kasashen Afrika suke kin samar da isassun kudaden da za a rika yin bincike mai zurfi game da kirkiro da rigakafin cutar a yankin Afrika.

“Magani kadai ake amfani da shi domin samun sauki idan mutum ya kamu da cutar kuma magungunan ma daga kasashen waje a ke shigowa da su.

Mataimakin shugaban kungiyar likitocin Afrika Ebuta Agbo ya ce kasashen Afrika musamman Najeriya ba su maida hankali wajen samar da wadatattun kudade domin kiwon lafiyar mutanen su.

Agbo ya ce a kasashen Afrika adadin yawan kudaden da gwamnati ke kashewa mutum daya domin kiwon lafiyar sa baya wuce Dala 8 zuwa 29 amma kuma a kasashen da suka ci gaba gwamnatin kasashen na kashe Dala 4,000 a kan kowani mutum daya ne.

“Sannan kuma babu isassun ma’aikata da za su rika kula da marasa lafiya kamar yadda ya kamata.

Bayan haka Olaniya ya kara da yin fashin baki game da yawan mace-mace da ake samu a yankin Afrika a dalilin fama da zazzabin cizon sauro da mutane ke fama da.

Ya ce zuwa yanzu Maleriya yayi ajalin yara da manya akalla 637,000 a duniya.

Olaniya ya ce Najeriya na daga cikin kasashen duniyan da ta fi fama da yaduwar cutar inda tun daga shekarar 2011 zuwa yanzu kasar ta kashe Dala biliyan 1.3 don yaki da cutar amma har yanzu cutar ta ci gaba da yaduwa a kasa kaman ba a taba kashe irin waɗannan kuɗade ba.