QATAR 2022: Jamus Ta Tsallake Rijiya Da Baya A Gasar Cin Kofin Duniya
Jamus ta gujewa wani abin kunya na ficewa daga gasar cin kofin duniya a farkon gasar a lokacin da suka tashi kunnen doki 1-1 da Spain a ranar Lahadi, inda Niclas Fuellkrug ya farke kwallon da ya ci a minti na 83 da fara wasa.