QATAR 2022: Ƙasashe 10 da su ka fi sauran ƙasashe tsadar ‘yan wasan cin Kofin Duniya

Yayin da ake shirin fara gasar lashe Kofin Ƙwallon Ƙafa na Duniya wato Qatar 2022 a ranar Lahadi, daga cikin ƙasashe 32 da za su fafata, PREMIUM TIMES Hausa ta tsamo ƙasashe 10 waɗanda jimillar tsadar ‘yan wasan su ya fi na sauran ƙasashen.

1. INGILA: €1.22 Biliyan:

Kasar Ingila wadda ba a sa ran za ta iya lashe kofin duk da ta zo na biyu a Gasar 2018, ta fi ‘yan wasa masu tsadar da sun kai fam na biliyan €1.22.

2. BRAZIL: €984 MILIYAN:

Brazil mai ‘yan wasan da tsadar su ta kai €984, ita ce ta biyu wajen yawan ‘yan wasa masu tsada.

3. FARANSA: €797 MILIYAN:

Ita ke da yawan ‘yan wasa masu tsada ta uku a ƙasashen da su ka je gasar cin Kofin Duniya a Qatar.

4. PORTUGAL: €794 MILIYAN:

Portugal ce ƙasa ta huɗu mai tsadar ‘yan wasa har jimillar €794 Miliyan. Bruno Fernandez ne mafi tsada a Portugal.

5. SPAIN: €724 MILIYAN:

Spain ce ƙasa ta biyar wajen tsadar ‘yan wasa har jimillar €724 Miliyan. Pedri ne ɗan wasan su mafi tsada na €82.

6. GAMUS: €671M

7. AJENTINA: €541M

8. BELGIUM: €498M

9. NETHERLANDS: €425M

10. URAGUAY: €355. Pede Velvade na Real Madrid mafi tsada a wannan ƙasar.