PDPn KADUNA A 2023: Tsakanin Isah Ashiru, Ramalan Yero, Shehu Sani da Sule Hunkuyi, An ya za a haifar da da mai ido kuwa?

Jam’iyyar PDPD a jihar Kaduna ta na gab da fadawa cikin mummunar rudanin da idan bata yi da gaske ba zai iya sa APC ta samu rabas, garas gasassa daga sama a zaben gwamnan jihar a 2023.

Ga dukkan alamu duka wadannan jigajigan PDP din sun fallo takubban su kowa ya jawo banten sa zai daura domin fafatawa a zaben fidda gwani tukunna kafin a tunkari zaben mai gaba daya.

A baya dai honarabul Isah Ashiru ke kan gaba wajen neman cira tutar jam’iyyar sai dai kuma dawowar sanat Shehu Sani jam’iyyar PDP da kuma bayyana ra’ayinsa na fitowa takarar gwamna Kaduna a Jam’iyyar PDP ya na neman ya dagula wa jam’iyyar lissafi. Sannan kuma ga tsohon gwamna Ramalan Yero shima ya ce wannan karon sai yaga abin da ya ture wa buzu nadi.

Akwai kuma jigon jam’iyyar wanda aka fisani da yanka daya wato Sule Hunkuyi wanda shima jigo ne a siyasar PDP.

Abin lura a nan shine anya acikin wadannan yan takara akwai wanda zai iya janye wa wani kuwa a wannan karo musamman ganin ba Nasir El-rufai bane zai yi takarar gwamna sai wanda ya zaba wato dan lelen sa.

Hakan ya sa kowa na ganin idan aka buga lissafi mai kyau akwai alamun PDP za ta yi tasiri fiye da yadda ta yi a baya.

Sai dai kuma zabi ya rage wa mutanen jihar Kaduna domin wasu na ganin dukkan su ba za su iya kada dan takaran APC ba wanda El-Rufai zai zabo musu dubi da irin ci gaban da aka samu a jihar Kaduna babu kakkautawa tun bayan darewar gwamnatin APC a 2015.

A wani gefen kuma babban abin tambaya da yin nazari a akai shine, shin mutan Kaduna a shirye suke su koma ga mulkin PDP ko kuma suna ganin salon mulkin El-Rufai da wanda zai tsayar musu yafi musu akan wadannan jerin ‘yan takara na PDP.