NUC ta kai ziyara jami’ar Franco- British, Kaduna ɗaya daga cikin jami’o’in da Farfesa Gwarzo ya kafa

A ci gaba da kara faɗada fannin ilimi da bunƙasa shi a Najeriya, Farfesa Adamau Gwarzo ya na dab da buɗe sabuwar jami’ar Franco-British dake Kaduna.

Jami’ar Franco British Kaduna, za ta zamo jami’a ta farko da za a rika karatu da harsuna biyu, Turanci da Faransanci wanda duk ɗalibin da ya kammala karatu a jami’ar zai goge a turanci da faransanci.

Ranar Asabar 28 ga Janairu, jami’an Hukumar kula da jami’o’in kasar nan, NUC karkashin jagorancin babban darekta a hukumar Dr Mustapha Rasheed, suka kai ziyarar gani wa ido atyukan da aka yi a jami’ar zuwa yanzu domin domin bata lasisin fara aiki.

Farfesa Adamu Gwarzo tare da makarraban sa suka zagaya da jami’an NUC din cikin makarantar.

Sun duba dakunan karatu da aka gina, Gidajen malamai, wurin cin abinci, da sauransu.

Bayan haka sun baiwa jami’ar wasu shawarwari da kuma yabawa da jinjina wa Farfesa Gwarzo bisa kokarin da yayi wajen ganin aiki a jami’ar ya kai wannan matsayi.

Jami’ar Franco- British na daga cikin jami’o’i 4 da Farfesa Gwarzo ya kafa.

Bayan wannan jami’a, akwai Jami’ar Maryam Abacha dake Nijar da kuma wanda ta ke Kano.

Baya ga haka gidauniyar sa na tallafawa jami’o’in kasar nan waɗanda ke mallakin gwamnatin Tarayya ne. Sannan kuma da taimaka wa mutane musamman ɗalibai wajen samun guraben karatu a jami’ar da wasu jami’o’in.