Mutum sama da biliyan biyu na fama da karancin ruwan sha a duniya – Majalisar Dinkin Duniya

Wani rahoton Majalisar Ɗinkin Duniya ya yi gargaɗin cewa duniya na cikin barazanar fuskantar ƙarancin ruwan sha saboda amfani da buƙatar ruwa sosai da ake da ita ga kuma matsalar sauyin yanayi.

“Duniya na cikin matsalar faɗa wa mawuyacin hali saboda yawan amfani da ruwa,” in ji rahoton.

Bisa ga labarin da BBC Hausa ya wallafa ashafinsa na yanar gizo ya nuna cewa an fito da wannan rahoto gabanin taron MDD na farko kan ruwa da ake yi tun 1977.

Sakatare Janar na UN Antonio Guterres, ya ce yanayin da ake samar da ruwa a yanzu ba mai ɗore wa ba ne, kuma wannan yanayin tamkar jinin bil Adama ne ke tsiyayewa saboda matsalolin ƙarancin ruwan da ɗumamar yanayi da gurɓatar muhalli ke ci gaba da haifarwa.

Babban editan da ya wallafa rahoton da aka kira da World Water Development Report wanda MDD ta kaddamar – Richard Connor – ya ce duniya na fuskantar gagarumar matsala.

“A halin yanzu, kashi 10 cikin 100 na al’umomin duniya na rayuwa ne a karkashin wani yanayi na matsanancin karancin ruwa.

“Rahotan ya nuna cewa kimanin mutum biliyan uku da miliyan 500 na fama da rashin wadataccen ruwa na tsawon wata daya a kalla cikin kowacce shekara.”