MUMMUNAN HARIN JIRGIN KASA: Har yanzu ba a san yawan wadanda ‘yan bindiga suka kashe ba, mutane na bayyana rasuwar ‘yan uwansu

Gwamnan Kaduna Nasir El-Rufai ya bayyana mika ta’aziyyar sa ga yan uwa da iyalan wadanda suka rasu a harin jirgin kasan Abuja-Kaduna wanda ya auku ranar Litinin.
Gwamnan ya ziyaci asibiti 44 da na St Gerard domin duba marasa lafiya da ke kwance ana duba su.
Bayan haka mutane da dama na saka hotunan ‘yan uwansu da ba a gansu ba har yanzu da wadanda aka kashe a harin.
Cikin wadanda aka bayyana rasuwarsu zuwa yanzu akwai wani babban darekta a hukumar NBTE Abdu Kofarmata wanda tuni har gawarsa ta isa Kano domin a suturtashi.