Muhimman Batutuwa 10 A Tattaunawar PREMIUM TIMES Da Sheikh Gumi

Sheikh Ahmad Gumi ba baƙon masu karatu ba ne. Wanda bai san shi ba a ƙasar nan a yanzu ba su da yawa, musamman bayan da ya yi kasadar riƙa shiga dazuka wurin ‘yan bindiga, domin ƙoƙarin ganin an kawo ƙarshen hare-haren da ke neman ya gagari magancewa a yanzu.

Kwanan nan Gumi ya ce ya janye hannun daga wannan ƙoƙari da ya ke yi, tunda Gwamnatin Tarayya ta ayyana ‘yan bindiga a matsayin ‘yan ta’adda, lamarin da ya ce ba hakan ne zai magance matsalar ba.

PREMIUM TIMES ta yi masa tattaki, ta tattauna da shi, kamar yadda za ku karanta tsakuren da aka fito da su daga ciki doguwar tattaunawar.

1. Tsakanin Gwamnati Da ‘Yan Bindiga: “Maganin da gwamnati ke ɗirka wa marasa lafiya daban, ciwo daban.”

Gumi ya shaida wa PREMIUM TIMES cewa, “kwata-kwata gwamnati ba ta ɗauko hanyar magance matsalar ba. Saboda cutar da ke damun lamarin daban, ita kuma gwamnati maganin da ta ke ɗirkawa daban. Ai idan ka na so ka magance cuta, sai ka fara binciken wace iri ce? Me ya haddasa ta? Wane magani ya kamata a yi amfani da shi? To da haka ne za ka yi nasara. Amma ba a riƙa ɗirka wa mai cuta maganin hannun magori ba.”

2. Masu Kiran A Kama Ni Ba Su Da Bambanci Da ‘Yan Bindiga:

Malamin ya ce duk masu kiran a kama shi, daƙiƙai ne. Ba su ma da bambanci da ‘yan bindiga.

“Ni ina bakin ƙoƙarin da na ke yi ne a gwargwadon fahimtar da na yi wa matsalar. Kuma a kan haka na ke bayyana ra’ayi na. Kowa na da ‘yancin na sa ra’ayin. To ta yaya za ka riƙa yi min Allah-wadai don fahimta ta da ra’ayi na ya sha bamban da naka?”

3. Batun Sojoji Sun Kasa Murƙushe ‘Yan Bindiga: Saboda an tura su aikin da su ne ya kamata a tura ba, ba aikin su ba ne.

4. Tun Da Buhari Ya Hau Ban Gana Da Shi Ba, Ban Yi Waya Da Shi Ba:

“Tabbas Buhari aboki na ne, kafin ya hau mulki na sha zuwa gidan sa mu na tattauna batutuwa da dama. Wannan kuma ba zai hana don ya hau mulki ya yi ba daidai ba, na ƙi nuna masa hanya ba.

Yayin da wannan matsala ta ‘yan bindiga ta ƙara muni, na yi ƙoƙarin ganin sa, amma ban yi nasara ba. To amma na janye jiki na yanzu kwata-kwata, tunda an ayyana ‘yan bindiga cewa ‘yan ta’adda ne, abin da ba shi ne zai magance matsalar ba.”

5. Batun Yi Wa ‘Yan Bindiga Afuwa Da Gumi Ya Nema:

“Lallai Ni matsaya ta kenan. Domin ko ba shi ne ainihin maganin ba, to hakan zai iya dakatar da barnar kafin a samu maganin dindindin. Yin afuwa zai sa a samar da kamar batun diyya, domin babu bangaren da bai yi asarar dukiya da rayuka masu yawa ba.

“Mun ga yadda yin afuwa ya yi tasiri ga ‘yan tawayen Neja-Delta. Kuma ya zama alheri ga tattalin arzikin Najeriya, saboda da aka yi masu afuwa sun ajiye makamai, sun bari ana haƙar ɗanyen mai a yankin su. Kafin hakan kuwa ai sojojin Najeriya sun kasa murƙushe su.”

6. Matsalar Dandazon Almajirai A Arewa: “Ba A Ƙwace Wa Makaho Sanda Sai Idan Wadda Ta Fi Ta Sa Za Ka Canja Masa:

“Ta yaya za a daina almajirci ko barace-barace a Arewa tunda ba a ɗauko hanyar gyara ba? Ai ba za ka raba makaho da sandar da ba, sai ga idan za ka musanya masa da wacce ta fi ta sa ne.

“Idan aka gina makarantu a garuruwan Arewa, sannan sai a kafa dokar hana gararambar almajirci. To ka ga an ɗauko hanyar magance matsalar kenan.

“Wanda ya yi ƙoƙarin magance wannan matsalar shi ne Goodluck Jonathan, domin shi ya yi hoɓɓasa ya gina makarantun tsangaya har guda 150 a Arewa. Amma da wannan gwamnatin ta zo, sai ta watsar da batun.”

7. Iri Shugaban Da Ya Dace ‘Yan Najeriya Su Zaɓa A 2023:

“Kada a tsaya batun karɓa- karɓa, duk shirme ne. Kada a kalli ƙabila ko yankin da mutum ya fito. A tsaya a zaɓi wanda ya cancanta, wanda zai iya haɗa kan Najeriya, wanda zai bunƙasa tattalin arzikin Najeriya, wanda zai samar da zaman lumana da saisaita ƙasar nan kan ƙasaitacciyar turba.”

8. Masu Ƙarajin Ɓallewa Daga Najeriya Daga Daƙiƙai Sai Jahilai:

“Masu kiraye-kirayen ɓallewa daga Najeriya daga jahilai sai daƙiƙai. Ta yaya a wannan zamanin da ƙasashe ke tseren zuwa sararin samaniya, kai kuma ka tsaya ka na fifita kabilar ka ko yankin ka? Wace tsiya ƙabilar ta ka ta tsinana? Wace amfana ake yi da ƙabilar ta ka?

9. Masu Cewa Ina Goyon Bayan ‘Yan Bindiga Kidahumai Ne:

“Ta yaya wanda ke ƙoƙarin kawo ƙarshen fitina a ce shi ke goyon bayan ta? Na saida raina na shiga cikin su, kuma an fara ganin tasirin abin kafin lamarin ya samu tangarɗa.

“Ni kai na an kama yaya na, sai da mu ka biya kuɗin fansa. An kama wani a masallacin mu, sai da mu ka biya kuɗin fansa. An kashe direban iyalan mu.”