MONKEY POX: Mutum 4 sun kamu a jihar Borno, mutum sama da 100 sun kamu a Najeriya

Ma’aikatar kiwon lafiya ta jihar Borno ta bayyana cewa mutum hudu sun kamu da cutar kurarraji na Monkey pox a jihar.

Shugaban fannin kiwon lafiyar jama’a Lawi Mshelia wanda ta tabbatar da haka ta ce hukumar NCDC ce ta gano mutum uku daga cikin mutum hudu din da suka kamu da cutar.

Sannan mutum daya din da ya kamu da cutar an gano shi a barin Biu.

Lawi ta ce wadanda suka kamu da cutar na killace a asibitin koyarwa na Maiduguri amma a makon jiya an sallami daya daga cikin mutum hudu din da suka kamu da cutar.

Hukumar NCDC ta ce daga ranar 4 zuwa 7 ga Yuly 2022 mutum 101 sun kamu da cutar a Najeriya.

Yaduwar cutar monkey pox a Najeriya

Hukumar NCDC ta bayyana cewa bana mutum 301 ne ake zargin sun kamu da cutar a Najeriya.

A shekaran 2017 an yi zargin mutum 88, mutum 49 a 2018, mutum 47 a 2019, 8 a 2020 da mutum 34 in 2021.

A jimmla adadin yawan mutanen da ake zargin sun kamu da cutar daga shekaran 2017 zuwa 2022 ya Kai 327.

A makon da ya gabata an samu rahoton cewa ana zargin mutum 56 sun kamu da cutar a jihohi 22.

Sakamakon gwajin da aka gudanar ya nuna cewa mutum 17 ne suka kamu da cutar a jihohi 12.

Mutum uku sun kamu da cutar a jihar Ondo, Adamawa -2, Bayelsa-2, Delta-2, Anambra-1, Borno-1, Edo-1, Gombe-1, Katsina-1, Kogi-1, Filato-1 da Legas-1.
NCDC ta ce tun bayan bullowar cutar a Satumba 2017 zuwa 10 ga Yuly 2022 an yi zargin mutum 813 sun kamu a jihohi 35

Sannan daga Satumba 2017 zuwa 10 ga Yuly 2022 mutum 11 sun mutu a jihohi shida a kasar nan.