Matafiya 193 sun yo wa Najeriya guzurin Korona

Akalla mutum 193 daga cikin mutum 2,357 da suka dawo Najeriya daga kasar Ukraine suka kamu da cutar korona.

Shugaban kwamitin PSC kuma sakataren gwamnatin Najeriya Boss Mustapha ya sanar da haka a taron da kwamitin ta yi da manema labarai ranar Litini a Abuja.

Mustapha ya ce an gano wadannan mutane sun kamu da cutar ne bayan gwajin cutar da ake yi wa duk matafiyan da suka dawo Najeriya daga kasashen waje.

Idan ba a manta ba kwanakin baya PREMIUMTIMES HAUSA ta buga labarin cewa mutum 60 da suka dawo Najeriya daga kasar Ukraine sun kamu da korona.

An gano wadannan mutane a gwajjn cutar da ake yi wa matafiyan da suka yi tafiya zuwa kasashen waje.

Yaduwar cutar

Alkaluman yaduwar cutar da hukumar NCDC ta fitar na ranar Litini ya nuna cewa mutum 87 sun kara kamuwa da cutar a jihohi biyar da Abuja.
Zuwa yanzu mutum 255,190 ne suka kamu da cutar.

Cutar ta yi ajalin mutum 3,142, mutum 249,476 sun warke a Najeriya.

Legas- 99,070, Abuja-28,588, Rivers- 16,624, Kaduna- 11,235, Filato- 10,247, Oyo- 10,215, Edo- 7,694, Ogun- 5,810, Delta- 5,364, Ondo-5,173, Kano- 4,978, Akwa-Ibom- 4,657, Kwara- 4,579, Osun-3,311, Gombe- 3,307, Enugu- 2,952, Anambra- 2,825, Nasarawa- 2,729, Imo-2,558, Katsina- 2,418, Abia- 2,116, Benue- 2,129, Ebonyi- 2,064, Ekiti-1 1,982, Bauchi- 1,939, Borno- 1,629, Taraba- 1,473, Bayelsa- 1,312, Adamawa- 1,203, Niger- 1,148, Cross Rivers – 823, Sokoto- 817, Jigawa- 667, Yobe-564, Kebbi-480, Zamfara- 375 da Kogi-5