Masu Kananan Sana’o’i Sun Bukaci A Samar Musu Matsuguni Idan Za’a Kore Su Daga Cikin Abuja

Biyo bayan kalaman da ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike, ya yi jim kadan bayan rantsuwar kama aiki na mayar da birnin kan taswirarta na asali, wasu masu kananan sana’o’i na neman a yi nazari kar a jefa su cikin matsin rayuwa.