MAI ARZIKI KO A KWARA YA SAIDA RUWA: Yadda kamfanin BUA ya ƙwace wa Nestle kambun gagara-gasa a hada-hadar kayan abincin masarufi

Cikin kwanaki bakwai kacal da shigar BUA Foods Plc cikin Kasuwar Hada-hadar Hannayen Jari a Legas, yanzu haka yanzu haka darajar kamfanin har ta ƙara ɗaukaka da kashi 59.1 bisa 100. Kamfanin kayan Abinci na BUA mai darajar hannayen jari Naira biliyan 720, a kan kowane hannun jari ɗaya Naira 40, yanzu ya zama sha-kundum, domin har darajar sa ta kai Naira tiriliyan 1.2, wato Naira 66 kowane hannun jari ɗaya kenan.

Tuni masana ƙabli da ba’adin hada-hadar hannayen ke ta mamakin irin yadda ake rububin hannayen jarin BUA Food Pls. Hatta masu zurfin bincike, manyan ‘yan tiredar hannayen jari da masu sa-ido sai hangame baki su ke yi cikin mamaki da al’ajabi.

BUA Food Plc: Sa’a Ta Fi Sammako:

BUA Food, wanda ya shiga Kasuwar Hada-hadar Hannayen Jari cikin Janairu, 2022, a cikin kwanaki shida ya shige gaban kamfanin kayan abinci na Nestle Nigeria, wanda reshe ne na Nestle S.A.

A yanzu BUA Food Pls shi ne na ɗaya a mafi girman Kamfanoni masu sarrafa kayan abincin masarufi a wajen ƙarfin jarin kasuwanci, bayan da jarin kamfanin BUA ya yi ƙaru da kashi 7.8.

Dama tun a cikin watan Disamba BUA Food Plc ya samu gagarimar karɓuwar kayan sa a kasuwa, irin su filawa, taliya, sugar, shinkafa da man girki. Dalili kenan waɗannan kayan masarufi suka shiga cikin sahun hada-hadar kasuwancin hannayen jari a matsayin ‘yan gida ɗaya kuma gurbi ɗaya, ba daban-daban ba.

Irin yadda kamfanin BUA Food Plc ya samu gagarimar kasuwa a Hada-hadar Hannayen Jari (Stock Exchange) a cikin wannan wata, a matsayin sa na sabon shigar kasuwar a karon farko, haka kamfanin BUA ya yi irin wannan mamayar shi ma shekaru biyu da suka gabata a kasuwancin hannayen jarin.

A wancan shekaru biyun, kamfanin BUA Cement da ya shiga hada-hadar ya na da darajar Naira 35 a hannun hannun jari ɗaya, a cikin shekaru biyu sai da darajar sa ta yi sama zuwa naira 85.

Abdussamad Rabi’u: Yaro Ɓata Hankalin Dare Ka Yi Suna:

Daga lokacin da hannayen jarin BUA Cement ya kai Naira 85, sai ga Shugaban BUA Cement ya tashi da kashi 77 na hannayen jarin, ya zama ƙasaitaccen attajirin da darajar nauyin aljihun sa ta kai dala biliyan 5.5. Jama’a, dala fa naira ba, kuma a cikin watanni 12 kacal.

Yayin da mashahuriyar Mujallar Forbes ta ɗaga Abdussamad Rabi’u a kasuwa, sai ga shi darajar sa ta kai shi ne mutum na shida da ya fi ƙarfin arziki a jerin attajiran Afrika baki ɗaya.

Kano Ko Da Me Ka Zo An Fi Ka: Kano, birnin da ya samar da Alasan Ɗantata, mutumin da a lokacin sa duk Afrika babu mai kuɗin sa, birnin ne dai ya samar da Aliko Ɗangote, wanda ya fito daga jinin Alasan ɗin, ko kuma a ce Alasawa. Aliko wanda a yanzu babu kamar sa a Afrika, kuma babu baƙar fatar da ya kai shi kuɗi a duniya, ya fito gari ɗaya da Abdussamad Rabi’u, wato Kano. Kuma duk haifaffun cikin birnin Kano ne.

Abdulsamad Rabi’u da ɗan sa Abdussamad Junior, su ke da kashi 99.8 na ilahirin naira tiriliyan 1.2 na hannayen jarin BUA Food Plc. Abdussamad Babba ke da kashi 88.9, ƙaramin ke da kashi 10. Sauran kashi biyu kuma ta sauran masu saka jari ce a kamfanin.