MAGANIN BABAN AISHA: Yadda jami’an NAFDAC suka yi wa kamfanin da ake hada maganin ‘Baban Aisha’ Diran Mikiya bayan PREMIUM TIMES ta bankado cakwakiyar da ke cikin hada wannan magani

Sanannen maganin Baban Aisha da ya karade musammam manyan birane a Arewacin Najeriya ya fada cikin tsaka mai wuya bayan PREMIUM TIMES ta bankado yadda ake hada maganin ba ta ingantaccen hanyoyi ba sannan kuma ba tare da samun lasisi daga hukumar NAFDAC ba.

Wakilin PREMIUM TIMES wanda ya yi bincike mai zurfi game da wannan magani ya yi tattaki zuwa wuraren da ake siyar da maganin, kuma ya gano cewa tun daga yadda ake hada maganin zuwa siyar da shi ba a bi ka’idojin hada magunguna ba duk da ko maganin gargajiya ce.

A lokacin binciken an gano cewa, hatta lasisin da hukumar NAFDA ta bashi a 2018 ya kare aiki, amma kuma masu kamfanin basu sabonta shi ba. Dalilin da ya sa aikin su ya haramta tun farko.

Mutane da dama na kwankwadar wannan magani da yake a cikin yar karamar robar magani. An yi makat lakabi da ‘sha yanzu, magani yanzu’. Domin a cikin tattar sa ma za ka ji yana kurin cewa kada mara lafiya ya kuskura ya garzaya asibiti domin robar maganin sa daya ya ishe shi, ya sha ya ji garau.

Sai dai kuma bayan binciken da aka yi sai aka gano, harkalla ce kawai masu kamfanin Baban Aisha suke yi, amma basu da lasisin hada irin wannan magani sannan kuma ma ita kanta maganin bayan bincike da aka yi an gano, tana da matukar illa da lahani ga lafiyar mutum muddum aka dage da shan sa.

A lokacin binciken mutane da dama da suka tattauna da wakilin mu sun shaida cewa suna amfani da wannan magani nashi matuka, amma kuma da dama daga cikin su sun ce kullun suka sha dai kamar jiya ne Iyau. Ba su jin wani gamsuwa a jikin su.

Wasu kuma sun ce su kan ji alamar sauki amma kuma ba mai dorewa ba. ” Saboda dai jiki ya saba da kuma dadin talla haka dai muke kwankwadar sa kullum ya buga kararrawar, baban Aisha, Bababn Aisha.

Shi ko Abdullahi, cewa ya yi ba shi da maganin da ya wuce maganin ‘Baban Aisha, a duk dolacin da na ji ba dadi a jiki na haka, ina jin wani zir-zir haka na kan nemi roban maganin baban Aisha guda daya ne in kwankwade shi sai na ji zan-zan.

NAFDAC ta yi diran Mikiya a Ofishin Hada Magani na Baban Aisha

Shugaban sashen gudanar da bincike a hukumar NAFDAC sun yi diran mikiya a kamfanin hada magani na Baban Aisha.

Ana tuhumarsa da hada magani ba tare da samun amintaccen lasisi daga hukumar NAFDAC ba, kazanta da wasu abubuwa dake da hadari ga lafiyar duk mashayin wannan magani.

A samamen da hukumar ta kai, an kama ‘HD injection polythene 25kg’ guda daya, ‘HDPE polythene 25kg’ guda daya, wasu buhuna masu suna akai, sikelin Hana big box, lasifika na tallar magani, kwalaben maganin da dai sauransu.

Akwai yiwuwar za a iya kama shi kansa Baban Aishan domin ya fuskanci tuhuma bisa kareraya doka da yayi wajen hada magungunan sa dake da hadarin gaske ga lafiyar mutane.