Likitoci sun yi nasasar yi wa wani mutum dashen zuciyar alade bayan tasa ta lalace

A cikin makon jiya likitocin asibitin Jami’ar Maryland dake kasar Amurka suka dasa wa wani maralafiya mai suna David Bennett Mai shekara 57 zuciyar alade baya ta sa ta lalace.

Fidar dasa wa Bennett zuciyar alade ya dauki tsawon awowi 8 kuma wannan aiki shine na farko da aka taba yin irin sa a duniya wato a dasa wa mutum dan Adam zuciyar Alade ya rayu da ita.

Kafin a shigar da shi dakin fidar Bennett ya bayyan wa manema labarai cewa dasa masa zuciyar alade itace mafita kamar yadda likitoci suka yi masa bayani idan ko ba haka zai mutu don tashi ta gama aiki.

Likitan da ya yi wa Bennett fidar Bartley Griffith ya ce kamfanin Revivicor dake Blacksburg Virginia ne suka bada gudunmawar zuciyar adalen da aka dasa wa Bennett.

Griffith ya ce kafin su dasa wa Bennett zuciyar sai da suka cire sinadarin dake inganta lafiyar alade guda uku sannan suka saka sinadarin amincewa da zuciyar idan ya shiga jikin mutum guda shida a jikin zuciyar.

A ranar 31 ga Disemba 2021 hukumar kula da ingancin abinci da magungun ta kasar Amurka ta amince a dasa wa Bennett zuciyar alade.

Griffith ya ce amincewa da zuciyar alade da Bennett ya yi ya bude hanya domin saka wa mutane wasu sassan dabobbi a maimakon na mutum wanda ke wahalar samu domin ceto rayukan su.

Shafin ‘organdonor.gov’ dake yanar gizo ya nuna cewa mutum 106,632 suke bukatar fidar zuciya inda a duk rana mutum 17 na mutuwa saboda karancin zuciyar mutane da ba a samu.

Zuwa yanzu likitoci sun ce Bennett na cikin koshin lafiya sannan zuciyar da suka saka mishi na aiki yadda ya kamata.