LAFIYA UWAR JIKI: An Samu Bullar Cutar Karambau A Agadez, Afirilu 2, 2023

Shirin lafiya uwar jiki na wannan makon yayi magana ne akan cutar karanbau da aka samu bullarta a jihar Agadez da ke jamhuriyar Nijar.

Wakilin Muryar Amurka Hamid Mahmoud ya zanta da likitan da ke kula da cututtuka masu saurin yaduwa na ma’aikatar kiwon lafiya ta Agadez Dr. Musa Hammadu game da batun.

Saurari cikakken shirin da Hauwa Umar ta gabatar: