KWALARA: Mutum 973 sun kamu, 17 sun mutu a Najeriya

Hukumar kula da hukumar babban birnin tarayya Abuja ta bayyana cewa wasu mutum 8 sun kamu da cutar kwalara.

Mai taimakawa ministan Abuja kan harkokin yada labarai Abubakar Sani ya sanar da haka a wani takarda da aka raba wa manema labarai ranar Juma’a da ya gabata.

Sani ya ce an gano wadannan mutane ne a dalilin gwajin jinin mutum 514 da aka yi ranar 8 ga Yuli 2021.

Jihar Ebonyi

Gwamnatin jihar Ebonyi ta bayyana cewa mutum 12 sun kamu sannan mutum 3 sun mutu a dalilin kamuwa da cutar a kauyen Amachi-Igwebuike dake karamar hukumar Ishielu.

Kwamishinan lafiya na jihar Richard Nnabu ya sanar da haka a makon da ya gabata.

Nnabu ya ce mutum uku sun rasa rayukansu ne a dalilin rashin zuwa asibiti da wuri.

Jihar Filato

Gwamnatin jihar Filato ta bayyana cewa mutum 953 sun kamu sannan mutum 14 sun mutu a dalilin kamuwa da cutar kwalara watanni biyu da suka gabata a jihar.

Kwamishinan lafiya Nimkong Lar Wanda ya sanar da haka ya ce zuwa yanzu an sallami mutum 910 daga asibiti sannan mutum 29 na kwance a asibiti.

Ya ce cutar ta fara bullowa a karamar hukumar Jos ta Arewa amma yazu cutar ta yadu zuwa kananan hukumomin 13 a jihar.

Yaduwar cutar kwalara a Najeriya

Idan ba a manta ba PREMIUMTIMES ta buga labarin cewa mutum 289 ne suka kamu da cutar a watan Janairu zuwa Yuni a kasar nan.

Hukumar NCDC ta ce an gano wadannan mutane a jihohi 8 a Najeriya.

Wadannan jihohi sun hada da Filato, Bauchi, Gombe, Kano, Zamfara, Bayelsa da Kaduna.

Hukumar ta ce zuwa yanzu cutar ta yadu zuwa jihohi 13 a kasar nan.

Matakan dakile yaduwar cutar da gwamnati ta dauka.

Domin dakile yaduwar cutar gwamnati ta hada hannu da masu ruwa da tsaki domin ganin an kara tsaftace ruwan fanfo da mutane ke samu a Abuja.

A jihar Ebonyi kuwa mutane dun yi kira ga gwamnati da ta samar musu tsaftacen ruwan sha.

A jihohin da cutar ta bullo gwamnati ta zuba ingantattun magungunan cutar domin kula da duk wadanda suka kamu da cutar kyauta.

Gwamnati na horar da ma’aikatan lafiya kan yadda za su kula da wadanda suka kamu da cutar tare da wayar da kan mutane hanyoyin guje wa kamuwa da cutar.

Daga nan gwamnati ta aika da ma’aikata domin gudanar da bincike kan yadda cutar ta bullo.

Hanyoyin gujewa kamuwa da cutar

1. Tsaftace muhalli.

2. Wanke hannu da zaran an yi amfani da ban daki.

3. A guji yin bahaya a waje.

4. Amfani da tsaftattacen ruwa.

5. Wanke hannu kafin da bayan an ci abinci.

6. Cin abincin dake inganta garkuwan jiki.

7. Yin allurar rigakafi

8. Zuwa asibiti da zaran an kamu da cutar.

likitoci sun yi kira da arika gaggauta garzaya asibiti domin warkar da cutar.