Kungiyar ma’aikatan kamfanonin samar da wutar lantarki ta kasa ta janye yajin aiki

Kusan duka manyan biranen Najeriya sun afka cikin rashin wutar lantarki ranar Laraba a dalilin soma yajin aiki da kungiyar ma’aikatan kamfanonin wutar lantarki ta kasa suka fara.
A jihohi kamar Kaduna, Legas, Oyo, Enugu, Babban birnin tarayya, Abuja da wasu birane, har zuwa cikin daren Laraba babu wutan lantarki a faɗin biranen.
Kungiyar ma’aikatan na bukatar gwamnatin tarayya ta cika musu wasu alkawurra da suka ɗauka musu ne sannan kuma da wasu bukatun musamman da ke gaban gwamnati kuma ta ki cikawa har yanzu.
Sai dai kuma a cikin daren Laraba ɗin kungiyar ta sanar da janye yajin aiki na tsawon makonni biyu.
A sanarwar januye yajin aikin da kungiyar ta yi, ta ce ma’aikatan kamfanonin samar da wutar lantarki. Za su koma aiki amma koma da sharaɗi.
” Gwamnati ta amince ta zauna da mu a duba bukatun mu. Kuma gwamnati ta ce gaba ɗaya abinda muke kuka akai za ta biya mana su cikin makonni biyu masu zuwa.