Kungiya mai zaman kanta ta horas da matasa 54 yadda ake dinka audugar mata da za a rika wankewa ana maidawa

Kungiya mai zaman kanta ‘Town Crier Initiative Africa’ ta horar da matasa maza da mata 54 kan yadda ake dinka adugan yin al’ada na mata a jihar Enugu.

Kungiyar ta kuma wayar da kan mata kan yadda za su tsaftace jikinsu a lokacin da suke al’adan su ta wata-wata.

Taron ya gudanar ranar Alhamis a garin Eungu.

Shugaban kungiyar Ogene Ogbodo ya bayyana cewa dinkakken audugan al’ada na da ingancin da wanda ake siyowa a kasuwa sannan yana da arha domin ana iya wankewa a kara amfani da shi.

“Idan aka wanke audugar sai a shanya ya bushe sai a goge da dutsen guga kafin a kara amfani da shi.

Ya ce dinka audugar al’ada dabara ce da zai taimaka wajen rage wa iyaye da mata kashe kudin siyan audugan al’ada.

Ogbodo ya yi kira ga gwamnati da ta rage farashin kudin audugan al’ada na mata saboda ba kowace mace ne take da kudin siyan auduga kowani wata ba.

Ya kuma kara yin kira ga gwamnati da ta saka wayar da kan mutane game da al’adan mace da yadda za ta kula da kanta a cikin darusan da ake koyar da dalibai a makaranta.

Ogbodo ya ce yin haka zai taimaka wajen rage nuna wa mata wariya da ake yi yayin da suke al’adansu na wata-wata.

Idan ba a manta ba a ranar Lahadi da ya gabata ne wasu kungiyoyin kare rajin dan Adam sun yi kira da a daina nuna wa mata wariya musamman a lokacin da suke al’adan su na wata-wata.

Kungiyoyin sun ce nuna wariya, talauci, canfe-canfen na cikin matsalolin dake hana mata da dama masaniyar yadda ya kamata su rika kula da kansu a lokacin da suke al’ada.

Kungiyoyin sun yi kira ga gwamnati da ta gidan dakin bahaya da Samar da ruwa domin dalibai mata su tsaftace kansu a lokacin da suke al’ada a makaranta.