Kotu ta yi wa gwamnatin Gombe da ‘yan sanda katanga da dan jarida, Dahiru Kera

Babbar kotu a jihar Gombe ta gargadi gwamnatin Gombe da ‘yan sandan cewa kada su kuskura su sake yi wa dan jarida Dahiru Kera barazanar kama shi ko kuma muzguna masa.
Idan ba a manta ba Kera ya shiga bakar littafin gwamnatim jihar Gombe ne tun bayan buga wata rahoto game da bashin da ake bin gwamnatin Yahaya Inuwa a jaridar Daylight Reporters wanda shine mawallafin wannan jarida.
A hukuncin da ya yanke kan karar mai lamba: GM/145M/2022, a makon jiya. Mai shari’a H. H Kereng na babbar kotun jihar Gombe ya gargadi gwamnatin jihar akan kama mawallafi jaridar, Dahiru Kera.
Kotun ta yanke hukuncin cewa gayyatar da aka yi da kuma barazanar kame mawallafin tauye hakkinsa ne; “Musamman idan aka yi la’akari da tanade-tanaden sashe na 34, 35, 39 da 41 na Kundin Tsarin Mulki na 1999 (kamar yadda aka yi wa kwaskwarima) da Yarjejeniya Ta Afirka kan ‘Yancin Bil Adama da Al’umma da kuma ayyana ‘yancin dan Adam na duniya.
Wannan nasara ne ga Kera wanda tun bayan wallafa wannan labari ya arce gudun tsira domin kauce wa barazanar gwamnatin Gombe da suka nemi a damke shi domin wannan labari da ya buga.
Kera ya daina zama a garin Gombe na wani lokaci mai tsawo kafin hukuncin wannan kotu.
‘yan jarida a Najeriya na fadawa tarkon ‘yan siyasa saboda wasu rahotanni da baiyi musu dadi ba.
Kera ya yi murnar wannan hukunci inda ya ce yanzu ya samu sauki tunda dama tun a farko ba laifi yayi wa gwamnatin ba.