Kotu ta yanke wasu ‘yan bindiga dake yin farfesu da kayan cikin mutane hukuncin mutuwa ta hanyar rataya

Kotun koli dake Fatakwal jihar Rivers ta yanke wa wani mai garkuwa da mutane hukuncin kisa ta hanyar rataya.
Kotun ta yanke wa Bestman Lekia da sauran mambobin kungiyar sa masu yin garkuwa da mutane wannan hukunci bayan ta kama su da laifin kisan mutum hudu sannan da amfani da hanjin mutanen da suka kashe suka yi farfesu da su.
Lekia da kungiyar sa sun rika aikata wannan ta’asa ne a kauyen Okwali dake karamar hukumar Khana.
Alkalin kotun Adolphus Enebeli ya ce ya yanke wa Lekia wanda aka fi saninsa da ‘Bigie’ wannan hukunci ne bisa laifukan da suka hada da fashi da makami, kisa, yin garkuwa da mutane da shiga kungiyar asiri.
Jaridar ‘Punch’ ya rawaito cewa Adolphus ya ce wadanda suka shigar da kara sun tabbatar wa kotu cewa Lekia ya aikata laifukan da ake zarginsa da su.
Ya ce a dalilin haka kotu ta yanke masa hukuncin kisa ta hanyar rataya wa Lekia.
Adolphus ya ce saboda irin halin da Lekia ya nuna yayin da kotun ta zauna ya tabbatar wa kotun cewa Lekia mugun mutum ne da ya kamata a rataye sa sau hudu ma, ya mutu sai hudu.
Sauran wadanda ake nema ruwa a jallo sun hada da Gbodu Nobaale, Etim Ekpe, Nenalebarri Mmeabe da Loveday Mmeabe.