KORONA: Ta yi ajalin mutum 5 mutum 144 sun kamu ranar Talata

Hukumar dakile yaduwar cututtuka ta kasa NCDC ta bayyana cewa mutum 144 sun kara kamuwa da cutar sannan wasu mutum biyar sun mutu a dalilin kamuwa da cutar.

NCDC ta ce akwai mutum 53 din da suka kamu da cutar daga jihohin Filato, Legas da Abuja daga ranar 15 zuwa 16 ga Nuwanba da aka hada a cikin mutum 144 din da suka kamu.

Banda yaduwa da cutar ke yi cutar ya ci gaba da kisan mutane a kasan.

Idan ba a manta ba daga ranar Juma’a zuwa Lahadi mutum 35 ne suka rasa rayukansu a dalilin kamuwa da korona.

A takanin wannan lokaci mutum 200 ne suka kamu da cutar a kasar nan.

Zuwa yanzu mutum 213,321 ne suka kamu, an salami mutum 206,206 sannan mutum 2,973 sun mutu a Najeriya.

Yaduwar cutar

Legas – 77,949, Abuja-23,431, Rivers-12,792, Kaduna-10,143, Filato-9,901, Oyo-9,867, Edo-6,599, Ogun-5,374, Kano-4,397, Akwa-ibom-4,338, Ondo-4,580, Kwara-3,999, Delta-4,096, Osun-3,016, Enugu-2,776, Nasarawa-2,517, Gombe-2,695, Katsina-2,317, Ebonyi-2,048, Anambra-2,346, Abia-2,029, Imo-2,174, Bauchi-1,776, Ekiti-1,778, Benue-1,863, Barno-1,344, Adamawa-1,136, Taraba-1,254, Bayelsa-1,248, Niger-1,056, Sokoto-796, Jigawa-611, Yobe-501, Cross-Rivers-662, Kebbi-458, Zamfara-348, da Kogi-5.

Shugaban kwamitin dakile yaduwar cutar korona ta kasa PSC Boss Mustapha ya bayyana cewa gwamnati ba za ta kara mai da hankali wajen ganin kowa da kowa musamman ma’aikatan gwamnati su yi allurar rigakafin cutar korona a kasar nan.

Mustapha ya ce gwamnati ta dauki wannan mataki ne ganin yadda rahotani suke nuna cewa korona ya ci gaba da yaduwa a wasu kasashen Turai saboda rashin yi wa mutane allurar rigakafin cutar.

Mustapha ya ce gwamnati za ta dauki matakain da za su taimaka wajen kamo wadanda suke da katin shaidan yin allurar rigakafin cutar ba tare da sun yi allurar ba.

Ya ce gwamnati ta samar da magungunan rigakafin korona da zai isa a yi wa mutum kashi 50% a kasar nan

Mustapha y ace nan ba da dadewa ba gwamnati za ta fara yi wa mutane allura da maganin da zai taimaka wajen kare mutanen daka kamuwa da korona