KORONA TA DAWO GADAN-GADAN: Mutum 1,332 sun kamu, uku sun mutu a cikin mako daya a Najeriya

Ga dukan alamu cutar Korona ta sake darkakowa Najeriya a zango ta biyar inda daga ranar 16 zuwa 23 ga Yuli mutum 1,332 sun kamu da cutar sannan mutum 3 sun mutu.

Hukumar dakile yaduwar cututtuka ta ƙasa NCDC ta gargaddi mutane kan ci gaba da kiyaye sharuddan gujewa kamuwa da cutar.

Zuwa yanzu mutum sama da 3,000 na killace a dalilin cutar.

Mutum 260,339 ne suka kamu da cutar sannan cutar ta yi ajalin mutum 3,147 a Najeriya.

A ranar Juma’ar da ta gabata shugaban WHO Tedros Ghebreyesus ya tabbtar cewa korona ta ci gaba da yaduwa a fadin duniya.

Ya ce sakamakon gwajin cutar da kungiyar ke samu na mako-mako ya nuna cewa adadin yawan mutanen da suka kamu da cutar a cikin makonni shida da suka gabata ya ninka yawan da ake samu sau biyu.

Ya ce nauin BA.4 da BA.5 dake karkashin nau’in Omicron ne ke yaduwa inda wasu daga cikinsu na da ingancin karya ingancin allurar rigakafin cutar a jikin mutum.

Ghebreyesus ya ce daga lokacin da cutar ta bullo zuwa 24 ga Yuli mutum 569,629,979 ne suka kamu sannan cutar ta yi ajalin mutum 6,383,438 a duniya.

Yaduwar cutar

NCDC ta bayyana cewa yi wa mutane gwajin cutar ya ragu zuwa Kashi 50% a Najeriya daga ranar 20 ga Yuni zuwa 3 ga Yuli.

Hukumar ta ce a tsakanin wadannan makonni kasar ta samu bakin mutane daga cikin kasan dake fita zuwa kasashen waje.

Daga ranar 19 zuwa 20 ga Yuli mutum 235 ne suka kamu inda daga ciki mutum 138 ne suka kamu da cutar a jihar Legas.

A ranar 23 mutum 619 ne suka kamu da cutar a kasar nan inda jihar Ekiti na da mutum 364, Legas-62 da Rivers -58.

A dalilin haka ya sa gwamnatin jihar Ekiti ta gargadi mutane jihar kan ci gaba da kiyaye sharuddan gujewa kamuwa da cutar domin a cikin makon gwamnati ta killace mutum 74 da suka kamu da cutar.

The NCDC noted that reported cases from Ekiti State include a backlog of 300 cases from August 2021 and 64 for June 2022.

Allurar rigakafin Korona

Jami’an lafiya sun Najeriya ta ƙasa yi wa mutum kashi 70% allurar rigakafin cutar kamar yadda WHO ta ce a yi domin dakile yaduwar cutar.

Shugaban WHO reshen Afrika Matshidiso Moeti ta ce kasashe biyu ne kadai a Afrika suka iya yi wa mutum kashi 70% allurar rigakafin cutar a kasashen su.

Ta ce wadannan kasashe sun hada da Mauritius da Seychelles sauran kasashen dake kokarin Yi wa mutum kashi 70% allurar rigakafin sun hada da Rwanda kashi 67% da Botswana kashi 64% sannan akwai akalla kasashe bakwai da suka yi wa Kashi 40% na mutanen su allurar rigakafin.

WHO ta bada wasu dabarun hanyoyi da za su taimaka wajen inganta yi wa mutane allurar rigakafin.

WHO ta ce yi wa jami’an lafiya Kashi 100% da Yi wa Kashi 100% na mutanen da basu da karfin karkuwan jikin kare su daga kamuwa da cutar zai taimaka wajen in ma burin yi wa mutum kashi 70% allurar rigakafin cutar.