KORONA: An samu karin mutum 1,125 da suka kamu, mutum 4 sun mutu daga ranar Lahadi zuwa Litini a Najeriya

Hukumar dakile yaduwar cututtuka ta bayyana cewa mutum 1,125 sun kamu da cutar korona sannan cutar ta kashe mutum hudu daga ranar Lahadi zuwa Litini a Najeriya.

Cutar ta ci gaba da yaɗuwa yayin da gwamnati ta fara yi wa mutane allurar rigakafin korona zango na biyu.

Idan ba a manta ba cutar ta kashe mutum 11 ranar Juma’a sannan mutum 8 a ranar Asabar.
Daga nan cutar bai sake kosher wani ba sai ranar Litini da mutum 4.

mutum 541 ne suka kamu ranar Lahadi sannan babu wanda aka rasa a ranan.

Jihar Legas-242, Akwa-ibom-94, Enugu-48, Oyo-48, Anambra-34, Rivers-19, Ogun-17, Ekiti-15, Abuja-9, Abia-5, Delta-2, Niger-1.
A ranar Litini mutum 584 sun kamu sannan mutum hudu sun mutu a jihohi 14 da Abuja.

Mutum 201 sun kamu a jihar Legas, Rivers-149, Abuja-82, Ondo73, Ekiti-17, Cross Rivers-13, Oyo-11, Ogun-9, Delta-8, Odun-8, Bayelsa-4, Kaduna-4, Kano-2, Kwara-2 da Sokoyo-1.

A jimla mutum 183,087 ne suka kamu, an sallami mutum 167,310 daga asibiti.
Mutum 2,223 sun mutu a kasar nan.

Allurar rigakafin korona zango na biyu

Idan ba a manta ba a ranar Litini ne gwamnati ta fara yi wa mutane allurar rigakafin korona zango na biyu.

Gwamnatin ta fara yi wa mutane allurar ne bayan ta karbi kwalaben maganin rigakafin korona na ‘Moderna’ guda miliyan 4 gudunmawar kasar Amurka.

Bayan haka gwamnati ta Kuma karbi kwalaben maganin rigakafin na ‘Johnson & Johnson’ guda 177,600.

Sannan nan ba da dadewa ba gwamnati za ta karbi kwalaben maganin Oxford-AstraZeneca guda 698,880.

Gwamnati ta ce za ta yi amfani da maganin wajen yi wa mutanen da suka yi allurar rigakafin zango na farko da Oxford-AstraZeneca.

Daga nan shugaban hukumar NPHCDA Faisal Shu’aib ya ce gwamnati za ta yi amfani da maganin rigakafin na ‘Moderna’ wajen yi wa mutane allurar rigakafi a wannan karo.

Shu’aib ya yi kira ga mutane da su ci gaba da kiyaye sharuddan gujewa kamuwa da cutar domin samun kariya.