Kin saka wa Ƙudirin Gyaran Dokar Zaɓe hannu da Buhari ya yi rahama ce ga talakawan Najeriya – Garba Shehu

Kakakin fadar shugaban Kasa Garba Shehu ya bayyana cewa makudan kudin da za a kashe wajen gudanar da zaben a kasar nan zai wuce misali idan har shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya saka hannu a kudirin gyaran dokar zabe da majalisa suka aika masa.

Shehu yace ganin irin wannan makudan kudade ne da za akashe ya sa shugaba Buhari ya maida wa majalisa da wannan kudiri cewa ba zai sanya mata hannu.

” Makudan kudaden da za a kashe a wurin gudanar da zabe musamman a wannan lokaci shine tashin hankali, domin kawai a gudanar da zabe. Maimakon haka aiki na ci gaba ya kamata ace an yi da su ba narka su a wajen zabe bakawai .

” Da farko dai kudin talakawa za anarka, kuma daga karshe masu kudi yan siyasa ne za su amfana da shi. Tsakani da Allah ba wannan lokaci bane Najeriya za ta yi gangancin narka kudi a siyasa kawai don amfanin wasu ba talakawa ba.

” A tuna fa a yanzu haka ma gwagwagwa ake ta yadda za a fito daga cikin wahalhalun matsalolin karayar arziki da annobar Korona ta kifar da muta ne ciki sannan kuma da matsalolin rayuwa, kawai kuma sai a sake kirkiro yadda za a zazzaga kudi talakawa a harkar da basu zai amfana ba.

A karshe Shehu ya ce ‘yan siyasa na wage baki ne kawai don amfanin su ba don talakawa ba, idan da gaske suke sun san gaskiya kuma su fito su yi ta kawai amma suna bin son rai.

Minista Abubakar malami

Ministan Shari’a kuma Antoni Janar na Tarayya, Abubakar Malami ya ce Shugaba Muhammadu Buhari ya ƙi sa hannu a kan Ƙudirin Gyaran Dokar Zaɓe ne saboda idan ƙudirin ya zama doka, matsalar tsaro ce za ta ƙara dagulewa a ƙasar nan.

Baya ga matsalar tsaro, Malami ya ce idan aka sa wa ƙudirin hannu ya zama doka, hatta siyasar Najeriya za ta riƙa yin tangal-tangal ne a dimokraɗiyyance.

Da ya ke bayani a wata tattaunawa da aka yi da shi a Gidan Radiyon Kano ta wayar tarho, Minista Malami ya ce, “sannan kuma dokar idan aka sa mata hannu za ta kasance sabon tsarin zaɓe ya yi tsadar gaske. Dalili kenan Shugaba Muhammadu Buhari ya ƙi sa wa ƙudirin hannu.” Inji Malami.

Shi dai wannan ƙudiri ɗauke ya ke da sabbin dabaru na fasahar inganta zaɓe, waɗanda idan da an yi amfani da su, to maguɗi zai yi wahala a zaɓukan ƙasar nan.

Sai dai duk da haka, Buhari ya da ƙafa ya tattake ƙudirin, ya ƙi sa masa hannu domin ya zama doka.

Idan ba a manta ba, Buhari a farkon hawan sa mulki ya yi alƙawarin gyara tsarin zaɓe a ƙasar nan bayan ya sha kaye a takara har sau uku a baya.

Babban abin da ya kawo tankiya a cikin sabon ƙudirin gyaran zaɓen dai shi ne batun yin zaɓen fidda-gwamnin jam’iyyun siyasa bisa tsarin kai-tsaye na ‘yar-tinƙe. Wato tsarin da za a ba kowane mamba na jam’iyya damar jefa ƙuri’a, maimakon tsarin wakilai da ake a kai yanzu, wanda gwamnoni ke saye wakilan jam’iyya (delegates).

Yayin da ake zargin cewa gwamnonin Najeriya ne su ka hure wa Buhari kunne ya ƙi sa wa dokar hannu, a yau kuma Minista Malami ya ce dokar idan an sa mata hannu ba ta wakilci ra’ayi ko haƙƙin ‘yan Najeriya mafi yawa ba.

“Ya kamata Ku sani Buhari a matsayin sa na shugaba, ya na da ‘yanci a kan dokokin ƙasar nan da su ka shafi siyasa, tattalin arziki, kasuwanci, tsaro da sauran su. Aikin shugaba shi ne ya yi la’akari shin dokar za ta iya ɗorewa sosai kuwa?”

“Saboda shugabancin ƙasa ba a kan siyasa kaɗai ya ta’allaƙa ba. Ya jiɓinci rayuwar jama’a da zamantakewar su, addinan su, tattalin arzikin su, tsaron su da lafiyar su da sauran su

“Su ‘Yan Majalisa sun damu ne kawai da makomar muƙaman su na siyasa da muradun su. Shi kuma Shugaban Ƙasa ya damu ne kan rayuwa da rayukan ‘yan Najeriya baki ɗaya, ‘yan siyasa da waɗanda ba ‘yan siyasa ba.” Cewar Malami.

Ya ce shi ƙudiri tilas sai ya fi yi wa mafi yawan al’umma fiye da miliyan 200 zama alfanu, ba wai wani ɗan ɓangare ne jama’a ba.

“A yau Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) na neman a ba ta naira biliyan 305 domin ta shirya zaɓen 2023. Shin yanzu idan har za a kashe waɗannan kuɗaɗen domin yin zaɓe, to nawa jam’iyyar APC za ta kashe idan za ta yi irin wannan zaɓen wajen fitar da ‘yan takara. Kenan aƙalla sai ta kashe naira biliyan 200. Saboda kowane ɗan jam’iyya zai jefa ƙuri’a kenan, maimakon a yi zaɓe a tsarin wakilan jam’iyya, wato ‘delegates’.