KASUWA A KAI MAI DOLE: Hada-Hadar Kasuwanci A Kasuwar Monkam Da Ke Kamaru – Yuni 4, 2023

Shirin Kasuwa na wannan makon ya kai ziyara kasuwar Monkam da ke yankin Littoral a kasar Kamaru, inda wakiliyar Muryar Amurka Maimounatou Sadou ta tattauna da masu saye da sayarwa a kasuwar. Galibi masu sayayya sun koka kan farashin kayayyakin masarufi da suka ce ya yi tashin gwauron zabi.

 Saurari cikakken shirin cikin sauti: