KARFIN HALI: Yadda Ɗan bautar kasa, NYSC ya damfari ƴan sanda naira 235,000

Kotun majistare dake Iyaganku ta gurfanar da dan bautan kasa mai suna Ukanwa Ikechukwu ranar Juma’a bisa laifin damfaran wata ‘yar sanda naira 235,000.
Rundunar ‘yan sandan jihar Oyo ta kai karar Ikechukwu kotu bisa laifin sata da karya.
A kotun Ikechukwu ya musanta laifukan da ake zargin sa da su.
Dan sandan da ya shigar da karar Olufemi Omilana ya bayyana cewa a ranar 4 ga Disembar 2022 da karfe 12 na rana Ikechukwu ya damfari ACP Modupe Okpaleke naira 235,000.
Omilana ya ce Ikechukwu ya karanta darasin ‘Physiotherapy’ a Jami’a sannan da ya zo bautar kasa sai aka tura shi aiki a asibitin ƴan sanda ‘Police Cottage’ dake Eleyele Ibadan.
“A wannan lokaci ne Ikechukwu ya hadu da Okpaleke wacce ke fama da rauni a kafa. Daga nan ne ya zolaye ta ya amshi kudi har naira 235,000 kudin keke zama.
Alkalin kotun M.I. Giwa-Babalola ya bada belin Ikechukwu akan naira 500,000 tare da gabatar da shaidu biyu a kotun.
Giwa-Babalola ya daga shari’a zuwa ranar 25 ga Mayu.