Karamar hukuma a Jigawa ta kori karuwai, ta rufe gidajen shan barasa

Karamar hukumar Gwaram a Jihar Jigawa ta baiwa karowan yankin dasu tattara su fice daga yankin cikin kwana talatin ko kuma su hadu da fushin hukuma.

Sanarwar ta shafi karuwai ne yan wasu jahohi amma karuwai yan Jigawa an basu dama su kawo mazajen aure domin a daura musu aure.

Shugaban Karamar hukumar Gwaram, Zaharadden Abubakar, ya bada sanarwar hakan a ranar Juma’a a lokacin wasu masu faɗa aji daga garin Sara suka kawo masa ziyara a ofishinsa dake Gwaram.

Shugaban ya kuma bada umarnin rufe gidajen shan barasa da gidajen rawa dake faɗin ƙaramar hukumar.

Abubakar yace anyi dokar ne saboda tsabtace yankin da kuma gyara tarbiyar mutane.

Ya kuma cewa Karamar hukumar ta Gwaram zata ɗauki nauyin aurar da tubabbun karuwai ƴan asalin Karamar hukumar idan har sun kawo mijin aure.

Abubakar yace an baiwa Yan Sanda da sauran jami’an tsaro umarni su kama duk wata karuwa dake cigaba da sana’ar karuwanci a yankin na Gwaram.