Kamar yadda suka saba, ‘Yan Kungiyar Shi’a sun halarcin zaman coci ranar Kirsimeti a Zaria

Domin taya kiristoci murnar zagayowar ranar Kirsimeti Kungiyar Shi’a a Zariya sun halarci taron coci daka ayi ranar a cocin Ekkelisiyar `Yan Uwa Ta Nigeria (EYN) .
Wannan ba shine karon farko ba da suke irin haka. A duk ranar kirsimeti mabiya kungiyar kan halarci zaman coci tare da kiristoci a Zaria domin taya su murnar ranar.
Da ya ke tattaunawa da ‘yan jarida bayan an tashi Coci, shugaban tawagar ‘yan shi’a din Isah Mshelgaru ya ce sun halarci zaman cocin na ranar Kirsimeti ne domin taya kiristoci murnar ranar Haihuwar Yesu.
Taron da aka yi a cocin Ekkelisiyar `Yan Uwa Ta Nigeria (EYN) dake Sabon garin Zariya ya samu halarcin mabiya akidar shi’a da dama sannan kuma bayan haka kungiyar ta baiwa cocin goron kirisimeti.
Faston cocin Tijjani Chindo ya mika godiyar sa ga bakin sa yana mai cewa yin haka zai kara dankon zumunci tsakanin musulmai da kiristocin yankin.
Daga nan sai kuma yayi kira ga sauran jihaohi da su yi koyi da irin haka domin samun hadin kai a koda yaushe.