Jiragen yaƙi sun yi luguden wuta a dazukan Sokoto da Katsina

Dakarun sojojin rundunar Operation Hadarin Daji sun kashe ‘yan ta’adda da dama tare da tarwatsa maboyar su a Dajin Sokoto da Katsina, a cewar rahoton PRNigeria.

A jihar Sakkwato, a yayin hare-hare da rundunar sojin saman Najeriya ta kai, ta farmaki dazukan Mashema, Yanfako, Gebe, da Gatawa da ke cikin ƙananan hukumomin Isah da Sabon Birni na jihar.

  • Jiragen yaƙi sun yi luguden wuta a dazukan Sokoto da Katsina
  • Atiku Abubakar na taya al’ummar Najeriya murnar shiga watan Maulidi

Wata majiyar soji ta shaida wa PRNigeria cewa an cimma wannan nasarar ne ta hanyar kai hare -hare ta sama da aka kai a ranar 5 ga Oktoba 2021, bayan jerin ayyukan sa -ido ta sama, inda aka gano wuraren.

“Mun gano inda ƴan bindiga daga sansanin Turji da Maigona da mayakansu ke haɗuwa don tsarawa tare da ƙaddamar da hare-hare.

“Dangane da haka ne, rundunar sojin sama ta shirya jiragen yaƙi masu sauƙar ungulu don afkawa wuraren. A cewar majiyoyi a yankin, jiragen saman sun kai hari a yankunan da aka nufa, inda suka tarwatsa wasu gine -gine tare da kashe wasu da yawa daga ‘yan bindigar.

Wasu mazauna garin sun hango waɗanda suka tsira daga hannun ‘yan ta’addan suna tserewa a wata makarantar firamare da ke ƙauyen Bafarawa.”

A jihar Katsina, PRNigeria ta tattaro cewa maboyar ‘yan ta’adda a yankunan dajin Rugu mai iyaka da Karamar Hukumar Kankara, jiragen rundinar Sojin sama sun yi luguden wuta tsakanin 30 ga Satumba zuwa 3 ga Oktoba 2021.

An tarwatsa sansanin ɗan ta’adda nan Gajere tare da kashe ƴan bindiga 34 a harin.

Haka kuma, kimanin mutane 20 da ake zargi suna daga cikin ƴan ta’addan sun samu munanan raunuka daban -daban.

An wallafa wannan Labari October 8, 2021 10:00 AM