JIKI MAGAYI: Bello Turji ya sako mutum 52 da ya yi garkuwa da su a jihar Zamfara

Kwanaki kaɗan bayan luguden wuta da sojoji suka riƙa yi a dazukan jihar Zamfara inda suka kashe shugabannin kungiyoyin ‘yan bindiga biyu da wasu mabiyansu a dajin Gusami, Bello Turji Wanda ya shahara a yin garkuwa da mutane da kan sa ya sako mutum 52 da ya yi garkuwa da su suna tsare wurin sa.

Turji ya saki wadannan mutane domin gwamnatin jihar Zamfara ta ɗau sassauta masa.

Wata majiya mai tushe daga fadar gwamnatin jihar ya tabbatar da haka wa PREMIUM TIMES a ranar Litinin.

Idan ba a manta ba PREMIUM TIMES HAUSA ta buga labarin wasikar da Turji ya rubuta kan a yi sulhu da shi sannan har da bada wasu sharuɗɗa da gwamnati zata bi idan tana son zaman Lafiya.

A cikin wasikar Turji ya gindaya wasu sharuɗɗa biyar da idan gwamnati ta cika su, shi ma zai dai na ta’addanci kisa da kama mutane da ya ke yi.

Farmakin da rundunar sojin sama ta yi a dajin Gusami na daga cikin sabbin matakan dakile aiyukkan ‘yan bindiga da rundunar ta dauka.

Sako mutum 52 da Turji ya yi.

Wani mazaunin karamar hukumar Shinkafi Mohammed Humility ya bayyana wa wakilin PREMIUM TIMES cewa mutanen da aka sako din an kama su ne a kauyukan dake kananan hukumomin Shinkafi, Zurmi da Birnin Magaji dake jihar Zamfara da wasu kuma kauyukan dake kananan hukumomin Isa da Sabon Birni a jihar Sokoto.

“Tun da safe muke sa idon ganin dawowarsu amma ba su iso ba sai da wajen karfe bakwai na dare sannan wani jami’in gwamnati ne ya yi shatan motoci biya da aka dauko mutanen daga bakin rafi.
Humility ya ce an kai mutanen garin Gusau.

Bayan haka wani mazaunin Shinkafi kuma babban malami a jami’ar Usmanu Danfodiyo Salihu Shinkafi ya ce ya tattauna da wani da ya yi ido hudu da mutanen da aka yi garkuwa da su ya ce ga dukkan alamu Turji ya sako wadannan mutane saboda rubdugun aman wuta sojin sama kryi da kuma dalilin kashe Alh Auta da aka yi nasaran yi.

Wani majiya daga fadar gwamnati ya ce gwamnati na da masaniya kan dalilin da ya sa Turji ya sako mutanen da ya yi garkuwa da su.

“Turji ya sako wadannan mutane ne domin faranta wa gwamnati bayan gwamnati ta yi watsi da wasikar da ya rubuto a kwanakin baya. Sai dai ba ni da tabbacin cewa hakan da ya yi zai faranta wa gwamnati rai ko a’a.