Jami’an tsaro sun ceto mutane 8 da mahara suka yi garkuwa da su a Kaduna, sun kashe ƴan bindiga 3

Kwamishinan tsaron jihar Kaduna Samuel Aruwan ya bayyana cewa jami’an tsaro a Kaduna sun ceto wadu mutane 8 da aka yi garkuwa da su a karamar hukumar Chikun.

Aruwan ya sanar da haka ranar Talata a wata takarda da ya raba wa manema labarai a garin Kaduna.

” Jami’an tsaro da ke aikin samar da tsaro a yankin Kaduna sun shaida wa gwamnatin jihar a wani rahoto cewa ma’aikata sun kashe ɗaya daga cikin ƴan bindigan da suka yi arangama da su a karamar hukumar Chikun wajen ceto wasu mutane 8 da suka yi garkuwa da.

Rahoton ya kara da cewa kamar yadda Aruwan ya bayyana ya ce bisa ga rahoton jami’an tsaro sun yi arangama da wasu mahara a Maraban Rido dake karamar hukumar Chikun

“Jami’an tsaron sun ji rukugin harbin bindiga sai suka ɗunguma zuwa wannan wuri.

“Jami’an tsaron sun bi sawun ‘yan bindiga inda suka ceto mutum takwas da aka yi garkuwa da su sannan suka cafke ɗaya daga cikin ‘yan bindigan.

Ga sunayen mutanen da aka ceto;

– Likita Igah
– Nancy Likita
– Genesis Likita
– Wilson Likita
– Mary Kalat
– Victor Joel
– Simon Musa Ali
– Rufus Elisha

Bayan haka jami’an tsaron sun fatattaki ‘yan bindiga yayin da suka kai wa mutane hari a kauyen Unguwar Tasha dake Birnin Yero a karamar hukumar Igabi.

“Jami’an tsaron sun kama mutum daya daga cikin ‘yan bindigan.

“Jami’an tsaron sun fatattaki ‘yan bindiga a Hayin Kanwa dake karamar hukumar Giwa sannan Kuma sun kama daya daga cikin ‘yan bindigan.

Kwamishinan ya bada lambobi kamar haka 09034000060 da 08170189999 da mutane za su iya kira idan suka ga wani ya zo da ciwo a kan kin sa na harbin bindiga.