Jami’an NDLEA sun kama Faston Coci da durum uku cike makil da muggan kwayoyi

Dakarun rundunar hukukar hana safara da ta’ammali da muggan kwayoyi ta kasa, NDLEA sun damke wani fasto mai suna Anietie Effiong da durum uku cike makil da hodar ibilis wacce suke kira Mkpuru Mmiri wanda aka yo masa safara sa daga kasar Indiya.
Kakakin rundunar Femi BabaFemi ya bayyana cewa an yi lodin kayan a mota kirar Bus daga unguwar Ojuelegba dake jihar Legas.
NDLEA ta kama motar a hanyar Umuahia – Ikot Ekpene, a lokacin da ake binciken motoci a wani shinge.
BabaFemi ya kara da cewa an gano cewa wannan dirum uku za a waske da su kasar Kamaru ne daga Najeriya.