‘INKONKULUSIB’: Yadda NNPP ta ƙwace kujerar Majalisar Tarayya ta Fagge daga hannun APC a Kano

Ɗan takarar majalisar tarayya na NNPP, Muhammad Shehu ya lashe zaɓen wakilcin Majalisar Tarayya na Ƙaramar Hukumar Fagge ta Jihar Kano.
Shehu ya kayar da wanda a yanzu haka ke kan kujerar zango uku a jere, Aminu Goro na APC.
Baturen Zaɓe Farfesa Ibrahim Suraj ya bayyana cewa Shehu ya samu ƙuri’u 19,024, shi kuma Sha’aibu Abubakar na LP ya samu 12,789.
Goro na APC wanda kuma shi ke kan kujerar, ya zo na uku da ƙuri’u 8,668.
A wani rahoton kuma, Alasan Doguwa, Ɗan Majalisar da ke tuhuma da kisan kai ya lashe zaɓen Tudun Wada/Doguwa a Kano.
Shugaban Masu Rinjaye na Majalisar Tarayya, Alasan Doguwa, kuma wanda ake zargi da laifin kisan kai a ranar zaɓe, Ado Doguwa, ya lashe zaɓen dabai kammalu ba, wanda aka kammala a ranar 15 Ga Afrilu.
Baturen Zaɓe Farfesa Sani Ibrahim, ya ce Doguwa ya samu ƙuri’u 41,573, shi kuma Yusha’u Salisu na NNPP ya samu 34,831.
An dai yi zaɓukan da ba su kammalu ba a mazaɓu takwas cikin Ƙaramar Hukumar Tudun Wada.
Wakilin ya ruwaito cewa an samu ruɗani da firgita masu zaɓe a zaɓen na wanda bai kammalu ba a ƙaramar hukumar.
Wannan ne karo na biyar da Doguwa zai wakilci ƙananan hukumomin biyu, kuma ya na ta mafarkin ganin ya zama Kakakin Majalisar Tarayya.
Rahotanni daga Kano sun tabbatar da NNPP ta ƙwace kujerar Majalisar Tarayya ta Ƙaramar Hukumar Fagge daga hannun Aminu Goro na APC.
Sannan kuma a Majalisar Dokokin Jihar Kano guda 40, NNPP na da 28.