INEC ta aika wa Buhari wasiƙa amincewa da Ƙudirin Gyaran Dokar Zaɓe

Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC), ta aika wa Fadar Shugaban Ƙasa wasiƙar da batutuwan da Kudirin Gyaran Dokar Zaɓe ya ƙunsa.

Sai dai kuma INEC ta shawarci Shugaba Muhammadu Buhari ya tuntuɓi jam’iyyun siyasa da ɓangarorin jami’an tsaro, dangane da kudirin da aka shigar cewa zaɓen ‘yar-tinƙi jam’iyyu za su riƙa yi a wurin zaɓen fidda-gwanin ‘yan takara.

A ranar 29 Ga Nuwamba ce Majalisar Dattawa ta aika wa Shugaba Buhari Ƙudirin Gyaran Dokar Zaɓe, wanda shi kuma a bisa doka, ya na da kwanaki 30 kacal da zai ɗauka ya sa wa ƙudirin hannu, domin ya tabbata doka kenan.

Shi dai wannan sabon ƙudiri, matsawar Shugaba Buhari ya sa masa hannu, to ya shafe Dokar Zaɓen ta 2010 kenan, wadda ita ce aka yi wa kwaskwarima.

A cikin kwaskwarimar dai an nemi a riƙa yin zaɓen ‘yar-tinƙi wajen fitar da ‘yan takara.

Sai kuma batun suka sakamakon zaɓe ta yanar gizo da sauran na’urori da kafafen sadarwa na zamani.

Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Ƙasa, Ibrahim Gambari ne ya rubuta wa INEC wasiƙa, inda ya nemi hukumar ta rubuto shawarwari ga Buhari, kan batutuwan da Kudirin Gyaran Dokar Zaɓe su ka ƙunsa.

Gambari ya shaida wa INEC cewa kada shawarwarin su wuce ranar 3 Ga Disamba.

Batun a koma yin zaɓen ‘yar-tinƙi wajen zaɓuka na fidda-gwanin takarar jam’iyyu ya haifar da ka-ce-na-ce a cikin jam’iyyar APC mai mulki. Yayin da ‘yan majalisa waɗanda mafi rinjaye ‘yan APC ne, su da ɓangaren Bila Tinubu ke goyon bayan ‘yar-tinƙe, su kuma yawancin gwamnoni sun fi so a bar tsarin yadda ya ke, wato wakilai tun daga mazaɓu har zuwa sama su riƙa yin zaɓen fidda-gwani.