IGIYAR KAWANCE TA TSINKE: APC ta ragargaji babban fasto Mbaka don ya ce Buhari ya gaza, ya sauka

Jam’iyyar APC ta ragargaji babban limamin Kirista, Ejike Mbaka, wanda bayan ya shafe shekaru ya na goyon bayan Shugaba Muhamamdu Buhari, a wannan karon kuma ya kware masa baya, ya ce ba ya iya samar da tsaro a Najeriya, don haka ya sauka kawai.

APC ta ce kalaman da Mbaka ya yi amfani da su sun yi tsaurin da za su iya haddasa tarzoma a kassr nan.

Kakakin APC Yekini Nabena, ya yi barazanar kai karar Mbaka a Babban Cocin Katolika, idan ya ci gaba da kinkimo danyar magana ya na dankara wa Gwamnatin Tarayya.

Mbaka wanda shi ne Shugaban Cocin Adoration Ministry da ke Enugu, kwanan nan ya yi kira ga Majalisar Tarayya ta tsige Shugaba Buhari idan ya ki sauka saboda ya kasa samar da tsaro a kasar nan.

Mbaka dai ya yi wannan furuci a cocin sa, inda ya yi kira ga fadar shugaban Kasa ta gaggauta kawo karshen matsalar tsaron da ta addabi kasar nan.

Yekini Nabena ya ce kamata ya yi Mbaka ya maida hankalin da wajen ibada a cocin sa, maimakon ya rika tsoma baki cikin siyasa, wadda babu abin da ya sani a cikin ta ko a wajen ta.

Ya kalubalanci Mbaka ya yi amfani fa cocin sa wajen yin addu’o’in neman zaman lafiya a kasar nan.

Ya nemi Mbaka ya yi koyi da Yesu Almasihu, wanda ya ce ya bi hukuma sau da kafa a rayuwar sa, har zakka ya rika biya.

Ya nemi Mbaka ya maida hankali a coci, ya kyale ‘yan siyasa su yi siyasar su.