HIMMA DAI MATA MANOMA: Yadda noman masara, waken soya da kashu ya karɓi matar da ta watsar da aikin banki

A jami’a, Bolanle Kayode ta yi digiri na farko a fannin tsarin noman tattalin arziki. Bayan ta kammala karatu, ta so yin aiki a manyan masana’antu na harkokin noma, ma ba ta samu ba, sai ta shiga aikin banki.

Bayan ta shafe shekara 23 ta na aikin banki, Bolanle ta yi hoɓɓasa biyu. Wato yin karatun digiri na biyu da kuma shiga harkar noma gadan-gadan.

A yanzu haka ta na noman masara da waken soya da kuma kashu a jihar Oyo.

“Wato da na fara harkar noma, farko dai tunani na shi ne noma ‘ya’yan itaruwa, saboda ba na son noman kayan abinci. Domin duk shekara sai ka yi ta gaganiyar noma da kaftu da sauran wahalhalu. Shi ya sa na tunanin na noma abin da sai bayan shekaru kamar biyar zai girma. Sai kawai na ci gaba da cin moriyar sa har tsawon rayuwa.

“To a cikin 2017 sai na fara aikin noman kashu. Na fara da noma kaɗan, saboda bai wuce eka 150 ba. Amma sai na ƙara lafta masara da waken soya a cikin gonar kashu ɗin, domin hakan ya fi riba. Amma dai na fara da eka 70 ta kashu.

“Wasu manoma na samu su ka kai ni inda na sayo irin kashu ɗin a kasuwar jama’ar karkara.

Da haka na fara, amma dai a fannin waken soya ne na fara shan wahala.

Takin zamani da iri babu matsalar samu k kaɗan, amma idan ka na da kuɗi. Sai dai ni ba na amfani da takin zamani wajen noman masara da waken soya. A ɓangaren kashu na ke amfani da takin zamani, saboda shi noman kashu jidali gare shi. Sai an yi shekaru ana kula da shi kafin a ci moriyar sa.

“Amma a wannan daminar zan yi wani noman gwaji daban. Zan ware wata gona na shuka masara wadda ke buƙatar takin zamani na riƙa zuba mata. Zan kuma shuka wadda na saba nomawa babu takin zamani.

Amma abin sai a hankali. Ka fahimci cewa Ni fa ba noman masara ɗin ko waken soya ne a gaba na ba. Ina noma su ne kawai domin rage zaman da na ke yi ina jiran shekarar da zan fara cin moriyar gonar kashu ɗi ta.

“Kashu ya fara amma ba sosai ba. Saboda lokacin ƙwarin sa ko ƙosawar sa bai yi ba tukunna. Amma nan da shekaru biyu zan samu yalwar sa sosai da sosai.”

Bolanle ya yi fatan a ce ta na da kamfani mai sayen masara da waken soyar da ta ke nomawa. Amma dai a yanzu cewa ta yi duk abin da ta noma, ana lodawa ne ana kaiwa kasuwannin ƙauye ana sayarwa.

Arangama Ta Da Makiyaya:

Lokacin da na fara noman kashu, ni na ɗauka shanu ba su cin ganyen kashu. Kuma tun kafin na fara noma gonar, na kan ga makiyaya na kiwo a filin.

“Lokacin da na shuka kashu, bayan ya fito sai makiyaya su ka banka shanu, su ka cinye min da dama. Ban daddara ba, ban ɗauki mataki ba, su ka dawo su ka sake cinye rabi.

“Cikin 2019 su ka banka wa gonar wuta. Haka cikin 2020. Na kai ƙara ofishin ‘yan sanda. Aka kamo iyayen su. Da na ce sai an biya ni miliyan 15, sai su ka kira ƙungiyar su. Aka yi ta ba ni haƙuri. A ƙarshe dai na sa aka rubuta yarjejeniya su ka amince cewa ba za su ƙara shigar min gona da shanun su ba.”