HEPATITIS: Akwai buƙatan gwamnaticin kasashen Afrika su zage damtse matuƙa domin kare jarirai daga kamuwa da cutar Hepatitis

Shugabar kungiyar kiwon lafiya ta duniya WHO reshen Nahiyar Afrika Matshidiso Moeti ta bayyana cewa rashin yin gwaji da yin maganin cutar Hepatitis na sa ana rasa akalla mutum 124,000 duk shekara a Afrika.

Moeti ta fadi haka ne ranan cutar Hepatitis na duniya da ake yi duk shekara domin wayar da kan mutane.

Cutar Hepatitis cuta ce dake kama huhu inda rashin gaggauta neman magani da wuri zai iya sa cutar ta rikiɗe ta zama dajin dake kama huhu.

Hepatitis cuta ce da ta zama annoba a Afrika inda a yanzu haka mutum miliyan 90 na dauke da cutar.
A yanzu Nahiyar Afrika na da kashi 26% daga cikin yawan mutanen dake dauke da cutar a duniya.

Bincike ya nuna cewa yara ƴan ƙasa da shekara biyar miliyan 4.5 na dauke da hepatitis B a Afrika.

Binciken ya nuna cewa Afrika na da kashi 70% daga cikin uwayen yara ƴan ƙasa da shekara biyar dake ɗauke da cutar a duniya.

Moeti ta ce kasashe da dama sun daƙile yaɗuwar cutar a jikin yara ‘yan ƙasa da shekara biyar zuwa kashi 1% amma har yanzu Nahiyar Afrika na baya da Kashi 2.5%.

Ta ce samar wa yara kariya daga kamuwa da cutar ya jaɗa da hana jarirai kamuwa da cutar tun suna cikin uwayen su sannan da yi wa yara allurar rigakafin cutar.

“Hakan zai tabbata ne idan an yi wa mata masu ciki gwajin cutar, yi wa yara allurar rigakafin korona da samar wa matan da suka kamu da cutar magani domin kare jariran dake cikinsu.

Moeti ta ce akwai kasashen Afrika 14 dake yi wa mata masu ciki gwajin cutar sannan da yi wa yara allurar rigakafin cutar.

A dalilin haka WHO ta yi kira ga sauran kasashen Afrika da su rika yi wa mata masu ciki gwajin cutar tare da yi wa yara kanana allurar rigakafin domin dakile yaduwar cutar.