GWANINTA KO GURGUNTAKA: Yadda malejin cinikayyar Najeriya ya riƙa rawa da ƙafa ɗaya cikin watannin Juli zuwa Satumba -NBS

Hukumar Ƙididdigar Alƙaluman Bayanai ta Kasa (NBS) ta bayyana cewa yayin aka samu ƙarin kayan da ake fitarwa zuwa ƙasashen waje ana sayarwa daga Najeriya tsakanin watannin Juli, Agusta da Sarumba, 2021, a gafe ɗaya kuma an samu ƙarin yawan kayan da ake shigowa da su.

Wannan sikeli na nufin hada-hadar cinikayya a cikin watannin bai yi wa Najeriya rinjayen da ya kamata ta samu ba.

NBS ta ce kayan da Najeriya ke fitarwa sun ƙaru da kashi 19.43 cikin Jiki zuwa Satumba, 2021.

A ranar Litinin ce NBS ta fitar da Ƙididdigar Watanni Uku na kusa da ƙarshen shekarar 2021.

NBS ta ce ƙarin kashi 10.43 da aka samu a cikin watannin Yuli zuwa Satumba, idan aka ɗora su kan na Afrilu, Mayu da Yuni da kuma kashi 58.59 aka kwatanta da watannin Yuli, Satumba da Oktoba, 2020.

“Hada-hadar cinikayyar Najeriya ta samu giɓi na naira biliyan 3,023.50, wato ya nuna ƙarin kashi 26.53 tsakanin waccan shekara da kuma wannan da mu ke ciki. Wato dai duk da ƙarin kasuwancin fitar da kaya waje da aka samu, kayan da ake shigowa da su sun rinjayi wanda ake fitarwa daga ƙasar nan.

Abin da kowace ƙasa ke so shi ne kayan da ake fitarwa daga ƙasar su kasance sun fi waɗanda ake shigowa da su yawa.”

“An shigo da kayan Naira biliyan 8,0153.77 cikin watannin Yuli, Agusta da Satumba. Yayin da adadin ya haura waɗanda aka shigo da su cikin watanni Afrilu, Mayu da Yuni yawa da kashi 17.32.

Kayan gonar da aka shigo da su ya ƙaru da kashi 21.01. Sauran kayan da yawan shigo da su ya ƙaru a watannin uku sun haɗa da kayan makamashi, albarkatun ƙasa kuda kayayyakin da aka sarrafa daga ɗanyen mai da su ka ƙaru da kashi kashi 34.60.

A fannin kayan da ake fitarwa daga Najeriya kuwa, an fitar da na Naira biliyan 5,130.30