Gwamnatin Neja ta bada kwangilar wani katafaren shatale-tale da zai ƙara ƙawata Minna

Gwamnatin Jihar Neja ta ba da kwangilar gina wani katafaren shatale-tale da zai sauƙaƙa zirga-zirgan ababen hawa wanda za ta kashe naira Miliyan 164.

Kwamishinan ayyukan jihar, Mamman Musa ne ya bayyana hakan a taron manema labarai a gidan gwamnatin jihar dake Minna.

Musa ya ce aikin faɗaɗa hanyar gidan gidan watsa labarai da aka bayar kwanan nan da kuma sabunta hanyar Imani Clinic zuwa Jonathan Palace ya sanya dole gwwmnati ta gina shatale-tale a mahaɗar hanyar dake kan babban titin Western Bypass don sauƙaƙa zirga-zirgar ababen hawa.

A wata takarda da babbar jami’ar watsa labarai na gwamnan jihar Mary Noel-Barje ta sanya wa hannu ta ce, Kwamishina Mamman Musa ya ce titin wani bangare ne na ƙoƙarin gwamnati na samar da ababen more rayuwa ga ‘yan jihar don sauƙaƙa zirga-zirgar su tare da ƙawata Babban birnin jihar.

Shima, Kwamishinan Filaye da Gidaje, Barista Mukhtar Nasalle ya bayyana cewa Majalisar Zartarwa ta Jihar a zamanta na yau Laraba ta amince da wani sabon tsarin gina sabbin gidaje da garuruwan masu kyau da za su taimakawa jihar wurin jawo masu saka jari.

Barista Nasale ya ce sabon tsarin da aka amince zai kuma taimaka wa Ma’aikatar sa wajen aiwatar da aiyyukanta ta yadda ya kamata.

Ya ce sabon tsarin da ya ƙunshi yadda za a sake tsara wasu birane da garuruwa masu kyau, waɗanda za su jawo masu saka jari daga ƙasashen waje zuwa jihar.

Kwamishanan filayen ya ce an samar da tsarin ne bisa tanadin dokar tafiyar da ma’aikatar.