Gwamnatin Kaduna za ta kashe naira biliyan 4 wajen tallafawa matalauta miliyan 2 – In ji Sani

Kwamishinan Kasafin kudi na Jihar Kaduna, Mohammed Sani ya bayyana cewa gwamnatin jihar za ta kashe naira biliyan 4 wajen tallafawa matalauta miliyan 2 a fadin jihar.
Hakan na kunshe ne a jawabin da kwamishina Sani yayi a wajen wani taron daliban jihar Kaduna dake jami’ar jihar Kaduna, KADSU ranar Alhamis.
” Yanzu a duniya matasa ne ke kan gaba. Matasa ake goga kafada da su wajen harkoki na ci gaba da suka hada da kimiyya da fasa ha da ake samu yanzu a duniya. Domin a samu nasara a shirin ci gaba na SDGs dole sai matasa sun maida hankali matuka wajen nuna kwarewa da sanin yakamata wajen damawa da su da ake yi domin ci gaba.
A jihar Kaduna karkashin gwamna Nasir El-Rufai, ana dama wa da matasa sosai wajen aiwatar da harkokin gwamnati. Cikin matasan da suka yi fice a wajen nuna bajintar su a jihar Kaduna sun hada da, Kwamishinan Kasafin Kudi na Jihar, Mohammed Sani, Kwamishinan Tsaro, Samuel Aruwan, Hafeez Bayero da dai sauran matasa.