Gwamnatin Kaduna ta dakatar da cin wasu kasuwannin mako-mako biyar a jihar

Gwamnatin jihar Kaduna ta dakatar da cin wasu kasuwannin mako-mako a kananan hukumomi biyar da ake fama da matsalar rashin tsaro a jihar.

Kananan hukumomin da dokar ya shafa sun hada da Birnin Gwari, Chikun, Giwa, Igabi da Kajuru.

Kwamishinan tsaron jihar Samuel Aruwan ne ya sanar da haka a wata sanarwa da ya fitar ranar Litinin a garin Kaduna.

Aruwan ya ce gwamnati ta kuma hana ‘yan bumburutu sayar da man fetur a wadannan kananan hukumomi.

Ya ce gwamnati ta yi haka ne bisa ga shawarwarin da hukumomin tsaro suka bata domin samar da zaman lafiya a jihar.

Aruwan ya ce an umarci jami’an tsaro su tabbatar an bi wadannan umarnin.

“Gwamnati ta yi kira ga mutane da su rika taimakawa gwamnati da bata hadin kai yayin da ake daukar matakan da suka dace wajen yaki da ‘yan bindiga da masu aikata miyagun laifuka a fadin jihar.

Aruwan ya ce layin wayar salulan jami’an tsaro a jihar a bude suke kullu: 09034000060 da 08170189999,”