Gwamnantin Neja na neman ƴan jihar su ƙarfafa zaman lafiya tsakaninsu domin ci gaba

Gwamnan jihar Neja Abubakar Sani Bello ya sake jaddada buƙatar ci gaba da zaman lafiya da haɗin kai domin ci gaban jihar.

Gwamna Sani Bello ya bayyana hakan ne jim kadan bayan ya idar da sallar juma’ar farko da aka fara yi a masallacin juma’a na gidan gwamnati.
Gwamnan ya sanar da cewa fara sallar juma’a a gidan gwamnatin zai taimaka waje sauƙaƙa wahalar ma’aikata da ke fita don yin sallar Juma’a a waje.
A nashi jawabi, shugaban ma’aikatan gidan gwamnatin jihar, Ibrahim Balarabe ya bayyana cewa gwamnati mai ci za ta ci gaba da yin wa’azi kan zaman lafiya a kowane lokaci, yana mai cewa saboda dalilan tsaro, sai an binciki masu shigowa gidan gwamnati daga waje kafin su samu damar Sallar juma’a a masallacin.
Tun da farko babban limamin masallacin Sheikh Mohammed Sani Abubakar yayin gabatar da hudubarsa ya yi ƙira ga dukkan al’ummar musulmi da su yi amfani da watan Dhulhijja don yin addu’ar ci gaba da zaman lafiya da ci gaban jihar da ƙasa baki ɗaya.
Masallacin juma’ar na gidan gwamnatin kafin yanzu masallaci ne na Khamsu-Salawat amma yanzu an ɗaukaka shi zuwa masallacin juma’a don yiwa dukkan al’ummar musulmi hidima a ciki da kewayen gidan gwamnatin.