Gwamnan jihar Kebbi ya yiwa mataimakinsa ta’aziyya

Mataimakin gwamnan jihar kebbi, Dr Sama’ila Yombe Dabai ya karbi baƙoncin Gwamnan jihar Abubakar Atiku Bagudu don yi masa ta’aziyar rasuwar babban ɗansa Ibrahim Sama’ila Yombe, da kuma hadiminsa Ibrahim Abubakar Boɗinga wanda ya rasu kwana biyu da rasuwan Ibrahim.

A wani jawabi da mai taimakawa mataimakin gwamnan kan harkokun sadarwa, Atom Turba Ishaku ya fitar, Ibrahim Sama’ila Yombe ya rasu yana da shekara 43 bayan fama da rashin lafiya a ƙasar Sudan yayin hadimin mataimakin gwamna, Ibrahim Abubakar ya rasu kwana biyu da bayan rasuwan rasuwan Ibrahim Yombe sakamakon mummunan hatsarin mota a hanyar Sakkwato zuwa Birnin Kebbi.
Ibrahim Abubakar, ya rasu yana da shekaru 36 ya bar mata 2 da yara 3.
Gwamna Bagudu ya yi addu’ar Allah ya jikan mamatan.
Gwamnan ya samu rakiyar Shugaban Ma’aikatan Gidan Gwamnatin, Alhaji Sulaiman Muhammad Argungu, masu ba gwamna shawara na musamman, Ibrahim Attahiru Tadurga da Ahmed Muhammed Kadanho. Kwamishinan Lafiya, Jaafar Muhammad Clean, Hon Bello Ka’oje da sauransu.